An dakatar da ‘yan majalisar dokokin jihar Zamfara 16 ne saboda barazanar tsige shugaban majalisar Bilyaminu Moriki a ranar Alhamis din da ta gabata.
‘Yan majalisu 7 daga cikin 24 na majalisar a zaman da suka yi da safiyar Litinin din nan sun dakatar da ‘yan majalisar.
‘Yan majalisar dai sun zargi takwarorinsu da kutsawa ofishin magatakardar majalisar da kuma sajan da ke hannunsu da wasu abubuwa da aka lalata a harabar majalisar.
Karin labari: Ariwoola ya rantsar da sabbin alkalan kotun koli 11
Majalisar karkashin jagorancin kakakinta Bilyaminu Moriki da safiyar Litinin din nan ta bayyana zaman majalisar da ‘yan majalisa 18 suka jagoranta a ranar alhamis din da ta gabata a matsayin haramtacce.
Mambobi 16 a karkashin jagorancin kakakin majalisar Pro-Tempo a yammacin ranar Alhamis din da ta gabata sun dakatar da kakakin majalisar Bilyaminu Moriki, saboda ya dade yana jinya a jihar, sakamakon sake bullar ayyukan ‘yan bindiga a fadin jihar.
Karin labari: Gwamnatin Benue ta bawa baƙin makiyaya mako 2 su fice daga jihar
‘Yan majalisar 7 a jawabansu daban-daban a zaman na ranar Litinin sun kuma zargi wasu jiga-jigan ‘yan siyasa a wajen jihar da daukar nauyin ‘yan majalisar 16 domin kawo cikas ga gwamnatin Gwamna Dauda Lawal.
Suna kira ga ’yan majalisar da abin ya shafa da dukkan mazauna yankin da su yi watsi da labarin da aka yi na cewa an dakatar da shugaban majalisar.
Wani dan majalisar wanda shi ne shugaban kwamitin da’a da gata ya yi kira da a gudanar da bincike kan lamarin kafin a dauki wani mataki.