Bayan shekaru bakwai da gwamnatin jihar Jigawa ta yi alkawarin samar da ‘Cibiyar Kiwon Lafiya Daya a kowacce mazaba’ a fadin mazabu 287 da ke jihar, har yanzu mazauna jihar na nuna rashin jin dadinsu kan rashin samun kulawar kiwon lafiya yadda ta kamata.
Bisa la’akari da kudaden da jihar ke samu, da kuma rahoton kasa-kasa a kananan hukumomi hudu da suka hada da Miga, Guri, Gagarawa, da kuma Birnin-Kudu, Elijah Akoji ya yi bayani kan yadda gwamnatin jihar ta gaza a fannin kiwon lafiya.
Jigawa
Tafiyar sa’a guda ce a babur akan titi mai tsawon kilomita 25 daga hedikwatar karamar hukumar Gagarawa zuwa mazabar Zarada inda Musa Sani mai shekaru 59 dake fama da ciwon suga ke zaune tare da danginsa.
Sani, uba ne ga ’ya ’ya 9 da mata biyu, wanda ke cikin matsanancin hali, lokaci bayan lokaci sai ya hau baburin Achaba zuwa cibiyar lafiya dake garin Yalawa wadda ke da nisan kilomita 9 domin a duba yanayin jikinsa tare da ba shi magani.
Domin saduwa da likita da kuma samun magungunansa, sai ya sake yin tafiya mai nisan kilomita 15 a kan babur zuwa babban asibitin Gumel da ke karamar hukumar Gumel a jihar Jigawa duk da rashin lafiyarsa.
Akwai cibiyoyin kiwon lafiya guda biyu kacal don Sani da sauran mazauna yankin da ke da cututtukan da ke fuskantar barazanar rayuwa.
Tsawon shekara 4 ke nan da Sani ya kamu da ciwon suga, inda yake fatan cewa za a kafa cibiyar kiwon lafiya a cikin al’ummarsa domin zata taimaka masa ya rage tafiya mai nisa don samun kulawar lafiya.
“Ina ziyartar cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta Yalawa a wani lokacin kuma babban asibitin Gumel akalla sau uku a mako, ina kuma zuwa ne akan baburin Achaba,” in ji shi.
“Lokacin da ba ni da kudi, sai in gangara zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Yalawa don duba hawan jini. Babban Asibitin Gumel kuwa ina ziyarta ne kawai saboda suna da likitoci.”
A wani bangare na alkawarin yakin neman zabensa a shekarar 2015, gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya yi alkawarin gina ingantacciyar cibiyar kiwon lafiya a dukkan mazabu 287 na jihar.
Gwamnati dai na ikirarin cewa ta cika alkawarin da ta dauka amma bayan shekaru da dama, har yanzu babu wani kwakkwaran abu na azo a gani lamarin da tuni ya dugunzuma hankalin jama’ar Kasa, da kuma fidda rai da abinda aka yi tsammani.
Wannan ba wai batanci bane ga al’ummar Jigawa, a don haka ne ma, ta ba da hoton yadda alkawuran yakin neman zabe da gwamnatocin baya suka yi a jihar Jigawa na sake fasalin fannin kiwon lafiya, da habaka hanyoyin samar da kiwon lafiya tare da rage kashe kudin da ake kashewa.
Abin bakin ciki, Sani daya ne kawai daga cikin wadanda ke fama da makamntan cututtuka sakamakon gaza cika alkawarin da gwamnati ta yin a “Zuba jarin Biliyoyin Naira a bangaren Lafiya “A ko wacce mazaba cibiyar lafiya daya.”
Mazabar Zarada da ke karamar hukumar Gagarawa, inda Sani ke zaune, ba ta da cibiyar kula da lafiya da za ta kula da lafiyar al’ummar yankin kusan 16,875.
Bayanai sun kuma nuna cewa cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko guda 6 ne kacal ke kula da mazauna yankunan da ke sassan mazabu 10 na siyasa dake karamar hukumar Gagarawa.
Kodayake wadannan cibiyoyin guda 6 suna aiki, sai dai babu isassun kayan aiki sakamakon fama da karancin kudi, da kuma rashin kyakkyawan tsari, tare da rashin likitoci tun lokacin da aka gina su tsakanin shekarun 2013 da 2016, kamar yadda binciken da jaridar Solacebase ta gudanar ya nuna.
Binciken SOLACEBASE ya kuma nuna cewa duk da cewa a matakin farko na kiwon lafiya kyauta ne a jihar Jigawa, cibiyoyin lafiya matakin farko din ba su da kayan aiki kuma ba su da ma’aikata, duk kuwa da kason da ake warewa a kasafin kudi na shekara, baya ga asusun samar da kiwon lafiya, da sauran tallafi daga kungiyoyi masu zaman kansu.
Mazabar Gyaiko inda ake amfani da babur a matsayin motar daukar marasa lafiya
A mazabar Gyaiko da ke karamar hukumar Birnin-Kudu, wata yarinya mai suna Bilkisu Isiayku ‘yar shekara 11 ta kusa rasa ranta bayan da maciji ya sare ta a gonar iyayenta, an garzaya da ita zuwa asibitin Bamaina, mai tazarar kilomita 15 daga mazabarsu a kan babur.
Iyayenta sun firgita matuka “Mun yi tsammanin za mu rasa ta, da ace muna da cibiyar kiwon lafiya inda za a iya ba ta maganin agajin gaggawa da ba ta kusa mutuwa ba, “in ji mahaifinta, Kabir Isiayku.
Mahaifiyarta mai suna Bilkisu Isiyaku ta ba da labarin irin yadda abin ya faru a lokacin da take shirin haihuwa watanni 7 da suka gabata.
“Mun saba amfani da babur don zuwa asibiti, yayin da nake shirin haihuwa watanni bakwai da suka gabata, da babur aka yi amfani aka kaini zuwa asibiti, na sha wahala sosai kuma na gode wa Allah da na haihu lafiya,” in ji ta.
Ga mafi yawan mata masu juna biyu a mazabar Gyaiko, suna jin dadin haihuwa a gida idan ba ta zo da tangrda ba, saboda nisan asibiti, da kuma hadarin hawan babur da yawan kudin da ake kashewa wajen neman magani.
Wani ma’aikacin kiwon lafiya na sa-kai a Gyaiko, wanda ya bayyana kansa a matsayin Hassan, ya shaida wa jaridar Solacebase cewa al’ummar yankin na fatan samun cibiyar Lafiya nan ba da jimawa ba, domin fita daga halin da suke ciki a halin yanzu.
“Ina sadaukarwa wajen taimakawa idan sun kawo mara lafiya gidana wasu lokutan kuma naje wurinsu, tun da ina da dan gogewa akan aikin jinya. Ba na yin wani abu da ya wuce abin da na sani kuma ina tura su asibiti idan bukatar hakan ta taso,” in ji Hassan.
Ahmed Danjuma shi ne Hakimin Gyiako, a yunkurin da yake wajen fitar da al’ummarsu daga halin da suke ciki ya taimaka wajen samar da fili don gina sabuwar cibiyar kula da lafiya a matakin farko domin amfanin al’ummar yankin. Ya shaidawa Jaridar Solacebase yadda al’amura suka kasance da kuma alkawarin da gwamnatin ta yin a zuba jarin makudan kudade tun a shekarar 2015.
“Mun yi namu bangaren, mun samar da fili domin gudanar da aikin gina cibiyar lafiya a yankin na mu. Muna fatan gwamnati mai zuwa za ta taimaka wajen duba irin kalubalen da al’ummar gundumar Gyaiko da kuma al’ummomi da dama da ke karkashin wannan gundumar ke fuskanta,” in ji shi, ya kuma kara da cewa cututtukan da ake iya magance su kamar zazzabin cizon sauro na ci gaba da lakume rayukan mazauna yankin.
Mazabar Agufa dake karamar hukumar Miga wata mazaba ce ta siyasa. Mazauna garin sai sun yi tattaki har zuwa hedkwatar karamar hukumar Miga mai tazarar Kilomita 15 ko karamar hukumar Jahun mai tazarar kilomita 25 sannan su sami cibiyar kiwon lafiya.
A mazabar Danmaganawa, da ke karamar hukumar Miga, mazauna yankin na neman taimakon gwamnati kan rage lokacin da ake batawa wajen neman lafiya.
“Har yanzu muna fatan wata rana gwamnati za ta kawo mana agaji. An sami adadin mace-mace da yawa sakamakon wannan mummunan yanayi. Mata masu juna biyu da ke shirin haihuwa da masu bukatar taimakon gaggawa, da wadanda suka yi hatsari ko kuma wata annoba, duk ana jigilar su ne a kan babur zuwa Miga ko karamar hukumar Jahun domin a yi musu magani ko haihuwa,” hakimin kauyen, Musa Muhammad, shi ne ya bayyana wa jaridar Solacebase.
Haka abin yake Guri, da Miga
Karamar hukumar Guri tana yankin santoriyar Jigawa ta arewa maso gabas inda aikin noma ne ya fi daukar hankalinsu. Kamar dai a karamar hukumar Miga, mazauna garin su kan yi tafiya mai nisa don neman lafiya.
Bukar Yerima shi ne Hakimin Guri. Ya koka da cewa mazauna gundumarsa, musamman mata masu juna biyu da yara har yanzu suna mutuwa saboda kananan matsalolin kiwon lafiya. Mazauna garin Guri, da makwabta irinsu TasgaYanma, da Arinjesko sukan yi tafiya zuwa garin Hadeja wanda bai wuce kilomita 13 ba don samun kulawar lafiya.
“A TasgaYanma, a zahirin gaskiya muna yin komai da kanmu ba tare da samun wani tallafi daga gwamnati ba. Muna tafiya mai nisan kusan kilomita 7 don debo ruwa. Mun gwammace yaranmu su yi noma tare da mu maimakon su yi tafiya mai nisa don zuwa makaranta. Muna tafiya har Hadeja ta hanyar Arinjesko don neman lafiya,” in ji shugaban kwamitin raya yankin TsagaYanma, Muhammad Alkali.
Da’awar karya ga al’ummar Jigawa
A cikin shekarar 2015, gwamnatin jihar ta yi alkawarin gina ‘Cibiyar Lafiya guda a ko wacce mazaba dake jihar’. A ci gaba da tunkarar zaben 2019, gwamnati ta yi jawabi ga manema labarai inda ta sanar da kammala aikin.
Binciken da jaridar Solacebase ta yi ya tabbatar da cewa ba haka ba ne kuma ya tabbatar da cewa gwamnatin Mohammad Badaru ta yi watsi da ikirarin da aka yi na yaudarar masu kada kuri’a yayin da suke neman tazarce a shekarar 2019. Har yanzu mazauna kauyukan dake yankunan Gagarawa da Miga da Guri da kuma Birnin-Kudu na fama da matsalar rashin samun kulawar lafiya.
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta kasha Naira Biliyan 12 a cikin shekaru 6 wajen gyara da gina cibiyoyin kiwon lafiya a jihar ciki har da gina Asibitocin PHC guda 287 a fadin jihar, al’amarin da babu gurbinsa.
Tallafin Kiwon Lafiya a Jihar Jigawa
Idan rabon tallafin da gwamnatin jihar Jigawa take yi wa fannin kiwon lafiya da gaske ne, ya kamata al’ummar karkara a jihar su ci gajiyar tallafin ingantaccen kiwon lafiya ba tare da tangarda ba.
Rahoton kashe kudi na ma’aikatar lafiya ta jihar ya nuna cewa an kashe kudi naira miliyan 85 da kuma kuma wata Naira miliyan 88 wajen inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a shekarar 2019 da 2020. Wannan kuma baya cikin Naira Biliyan 12 da ake zargin gwamnati ta kashe a shekarar 2018 da makamantansu.
Sai dai a shekarar 2021, alkaluman kashe kudaden gwamnatin jihar sun nuna ma’aikatar ta kashe sama da Naira Miliyan 600 wajen samarwa da inganta ababen more rayuwa da samar da ayyuka kamar yadda Bankin Duniya ya tallafawa shirin kiwon lafiya na ‘Cetar da rayuka miliyan daya (wato Saving One Million Lives) wadda shirin ya mayar da hankali kan bunkasa kiwon lafiya na matakin farko a fadin jihar.
A watan Disambar 2017, gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani asusu na lafiya na Naira biliyan 28 da aka kaddamar da nufin farfado da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a fadin kasar nan. A cewar hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa, jihar Jigawa na daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin.
Domin cika dokar kula da lafiya ta kasa, ta shekarar 2014, an ware Naira biliyan 55 a karkashin asusun samar da kiwon lafiya daga tushe, BHCPF da gwamnatin tarayya ta yi a shekarar 2019, Jihar Jigawa na cikin jihohi 15 na farko da aka fara gwajin. Asusun BHCPF na nufin samar da kudaden shiga da inganta ayyukan kiwon lafiya a mtakin farko. Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta sanya idanu wajen ganin an yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace. Sai dai babu wani abu da ke nuni da cewa an kashe kudaden ne bisa ka’ida a jihar Jigawa.
Gwamnati ta mayar da martini tare da kore zargin
Duk da cewa gwamnati ta hannun ofishin mataimakin gwamna ta dauki nauyin alkawarin da aka yi na ‘Duk Mazaba Daya za a samar da Cibiyar Kula da Lafiya Daya’ a shekarar 2015, Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jigawa, Dakta Kabir Aliyu, ya karyata wannan ikirari, inda ya musanta zargin.
“Gwamna bai yi alkawarin cewa zai gina cibiyoyin lafiya a kowacce mazaba dake fadin jihar ba. Shirin samar da Cibiyar lafiya ta ‘One Ward One Health Centre’, bibiya ce kawai a kan wa’adin da shugaba Buhari ya dauka na gina sababbin cibiyoyin lafiya 10,000 a duk sassan Najeriya,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “Idan kun san halin da hukumar kula da lafiya a matakin farko din mu ke ciki kafin karbar mulki, za ku fahimci yadda wannan gwamnati ta yi aiki sosai. Gwamnati ta yi nata aikin kuma babu cikakken tsari a ko’ina, don haka dole ne mu baiwa gwamnati goyon baya wajen sauya fasalin cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na jihar.
“Abin da gwamnati tace shi ne zata yi aikin farfado tare da gyara cibiyoyin, amma gwamnati ba ta yi amfani da kalmar ginawa ba,” in ji shi a wata hira.
Mukaddashin kwamishinan kuma babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa Dakta Salisu Mu’azu ya tabbatarwa da babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar Jigawa cewa.
“Jihar Jigawa tana da mazabun siyasa guda 287, domin a daidaita rahoton ku, ku zagaya dukkan mazabun sannan ku yanke shawarar cewa, ba za ku iya kammala ziyarar kananan hukumomi 3 da mazabu 6 na siyasa ba, kuna so mu dauki rahoton ku da wasa.”
“Gwamnati ta yi iya bakin kokarinta kuma ta sake fasalin cibiyoyin lafiya a jihar Jigawa. Idan ka kwatanta jihar Jigawa da sauran jihohi, na san za ka ga bambamci sosai,” inji shi.
Masana sun bayyana cewa Cin hanci da rashawa ne a kunshe cikin karya kawai a wannan lamari
Masana dai na ganin cewa cin hanci da rashawa a fannin kiwon lafiya na daya daga cikin munanan laifuka da dabi’u da kowace gwamnati ke yi.
“Idan aka dubi irin halin kunci da talauci a jihar Jigawa, da kuma yadda yanayin cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko suke, za ka iya yi wa mutanen Jigawa kuka,” in ji Dakta Ibrahim Galadima, wanda ya kafa wata kungiya mai zaman kanta ta Health Aid, tare da ayyuka a Arewa maso Gabas.
“Abin takaicin shi ne, da dukkan kudaden da aka samu daga kasafin kudi da kuma kungiyoyin bayar da tallafi, ya kamata jihar Jigawa ta kasance cikin jihohi biyar da ke da ingantattun cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko.”
“Na yi aiki a jihar Jigawa a matsayin mai ba da shawara a hukumar UNICEF a shekarar 2019, a wannan lokaci mun ziyarci cibiyoyin lafiya da dama a jihar, idanunka zasu zubar da hawaye sakamakon rashin ma’aikatan lafiyada wadataccen magani, domin aikin awon ciki sai an jira gogaggiyar ma’aikaciyar jinya ta zo daga Dutse, babban birnin jihar,” Galadima ya kara da cewa.
Dakta Bamidele Ajayi, sakataren kungiyar farar hula da ke yaki da cin hanci da rashawa, ya jaddada cewa cin hanci da rashawa shi ne mugunyar dabi’ar da ya kamata a kawar don samun tsarin kiwon lafiya mai inganci,
“Babu shakka, duk kudaden da aka ce an kashe sun riga sun kasance a asusun sirri. Fannin lafiya wani sashe ne kamar ilimi wanda dole ne gwamnati ta ba da fifiko tare da bibiyar yadda ake sarrafa kasafin kudinsa.
“Alkawura ne aka dauka kuma dole ne a cika su. Na tabbata a kan haka ne al’ummar jihar Jigawa suka zabi gwamnati, sun fahimci muhimmancin alkawarin da aka yi musu na ‘Samar da cibiyar Lafiya Guda a kowacce Mazaba’ domin akwai bukatar hakan a gare su.”
An gudanarda wannan bincike ne tare da tallafin cibiyar Wole Soyinka Centre for Investigative Journalism (WSCIJ) karkashin hadin gwiwar Media Engagement for Development, Inclusion and Accountability project (CMEDIA) wanda Gidauniyar MacArthur ta tallafa.