Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya soki masu suka a kansa, yana mai cewa waɗanda suka zarge shi da goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu yanzu su ne suka koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Wike, mai shekaru 57, ɗan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ne, amma yana aiki a cikin gwamnatin tarayya da ke ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar APC tun daga shekarar 2023.
Duk da cewa bai bayyana ficewarsa daga PDP ba, Wike ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar Tinubu a zaɓen 2023, inda jihar Rivers ta kawo masa ƙuri’u.
Yayin da yake kaddamar da aikin gina babban titin “outer southern expressway” a birnin Abuja, Wike ya bayyana cewa wasu gwamnoni da suka soki shi a baya saboda suna zargin yana lalata jam’iyyar PDP da taimaka wa APC, yanzu su ne suka bi sahunsa suka koma jam’iyyar mai mulki.
Ya ce ya kamata ma su yaba masa saboda kyakkyawan aikin da ya yi na buɗa musu hanya zuwa APC.
Ya bayyana cewa tarin sauya sheƙa daga manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP zuwa APC ya tabbatar da cewa goyon bayansa ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnati mai ci ya yi daidai, domin waɗanda suka soki shi a da yanzu sun zama mambobin jam’iyyar APC.
A cikin makonnin baya-bayan nan, siyasar ƙasar ta ɗauki salo na sauya sheƙa, inda gwamnoni da dama daga PDP suka bar jam’iyyar.
A ranar Talata, gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC tare da kwamishinoni, shugabannin ƙananan hukumomi 17 na jihar da kusan kashi 80 cikin 100 na shugabannin PDP a jihar.
Bayan sa, gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, shima ya sanar da barin PDP, kodayake bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba.
A cikin watanni shida da suka gabata, PDP ta rasa gwamnoni huɗu da suka hada da Sheriff Oborevwori na Delta, Umo Eno na Akwa Ibom, Peter Mbah na Enugu, da kuma Duoye Diri na Bayelsa.
Sauyin sheƙa na waɗannan gwamnoni ya ƙara nuna irin rikicin cikin gida da ke ci gaba da lalata jam’iyyar PDP a fadin ƙasar, yayin da wasu ke ganin APC na ƙara ƙarfafa matsayinta a siyasar Najeriya.













































