Tinubu ya aikewa majalisar dattijai shirinsa na tura rundunonin sojoji Niger

0

Shugaban kasa Bola Ahamed Tinubu ya aikewa majalisar dattijai shirinsa na aike da rundunonin sojoji Niger domin murkushe wadan da sukai juyin mulki.

Shugaban majalisar datijai Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar da Tinubun ya aike da ita ranar juma’a.

Wani bangare na wasikar yace” Sakamakon yanayi mara dadi da kasar nijar take ciki, bayan juyin mulki da sojoji sukai, kungiyar ECOWAS a karkashin mulkina tayi alla wadai da wannan juyin mulkin.”

“ECOWAS ta kuma dau tsauraren matakai akan kasar ta Nijar, sanan kuma zamu tura rundunar sojoji kasar domin tabbatar da zaman lafiya da kuma dawo da demokradiya” Inji Wani bangare na wasikar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here