Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawar sirri da wasu tsoffin jigan-jigan jam’iyyar PDP 2 a Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja.
Mista Anyim da Metuh, waɗanda duk sun riƙe mukamin Sakataren watsa labaran PDP na ƙasa, sun isa fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 1:30 na rana kuma suka wuce kai tsaye zuwa ofishin Tinubu.
Idan baku manta ba a kwanakin baya, Olisa Metuh, ya sanar da cewa ya yi ritaya daga siyasa kuma ya fice daga jam’iyyar PDP.
Karin bayani na nan tafe…