PDP: Mutfwang ya nesanta kansa daga korar Wike, Fayose da wasu

GOV. Mutfwang

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya nesanta kansa daga korar Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, da tsohon sakataren jam’iyya na ƙasa, Samuel Anyanwu, da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP.

A cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulɗa da jama’a na ofishinsa, Gyang Bere, ya fitar da yammacin Asabar, Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa ba a tattauna batun a taron gwamnonin PDP ko a zaman kwamitin koli na jam’iyyar, NEC na kafin gabatar da shi, tare da jaddada cewa kudurin bai nuna matsayarsa ba.

Gwamnan ya bayyana wannan yunkuri a matsayin wanda bai dace da lokaci ba, inda ya ce korar manyan jiga-jigai a wannan lokaci mai sarkakiya na iya lalata ƙoƙarin da ake yi na daidaita jam’iyyar, kuma hakan na iya ƙara zurfafa sabanin cikin gida da kuma kawo cikas ga cigaban sake fasalin jam’iyyar.

Ya ce dole jam’iyya ta fifita sulhu fiye da takaddama, tare da nuna cewa rikice-rikicen cikin gida mafi dacewa an warware su ta hanyar tattaunawa mai ma’ana da haɗin kai tsakanin ɓangarori.

Gwamna Mutfwang ya tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da goyon bayan duk wani mataki da zai kawo zaman lafiya, haɗin kai da gyara a cikin jam’iyyar PDP.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here