Pantami ya jagoranci kaddamar da sabon Masallacin da aka gina a Cibiyar PRNigeria Centre da ke Abuja

Prof Isa Ali Pantami Mallam Yushau Shuaib with other Patrons of the mosque 750x430

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya jaddada rawar da masallatai da dama ke takawa a matsayin masu samar da ci gaban kasa, bayan babbar rawar da suke takawa ta wajen yin ibada.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da sabon masallacin da aka gina a cibiyar PRNigeria a Wuye da ke Abuja, Pantami wanda malamin addinin musulunci ne kuma farfesa a fannin tsaro da harkokin Internet ya bayyana muhimmancin tarihi na masallatai a matsayin wuraren koyo, bunkasa halaye, kasuwanci, karfafa hadin kai, halaye masu kyau, da ci gaban al’umma da kuma tsara dabarun rayuwa.

Malam Yushau Shuaib, shugaban kamfanin na IMPR, masu buga jaridar PRNigeria, Economic Confidential, da sauran kafafen yada labarai ne suka gina masallacin.

Bikin kaddamar da masallacin ya samu halartar shuwagabannin al’umma, malamai, da masu fada aji.

Karanta: Majalisar Malaman Kano ta yanke hukuncin kan danbarwar masallacin Sahaba dake kundila

Farfesa Isa Pantami ya gabatar da wa’azi bayan Sallah a Masallacin tare da huduba.

Ya kara da bayyana yadda duniya ta amince da masallatai a matsayin cibiyoyin ilimi, inda ya bayyana jami’ar Qarawiyyin da ke kasar Maroko-wanda aka kafa sama da shekaru 1,200 da suka gabata a matsayin jami’a ta farko a duniya, da kuma jami’ar Al-Azhar da ke Masar, jami’a ta biyu mafi tsufa a duniya, inda ya ce dukansu cibiyoyi ne da suka samo asali daga masallatai kuma UNESCO ta amince da su saboda gudummawar da suke bayarwa ga ilimi da ci gaba.

A yayin taron, Pantami ya kuma yaba da yadda ake kiyaye Al-Qur’ani mafi dadewa a masarautar Ilorin, wanda ya cika shekaru sama da 200. Al-Qur’anin wanda mai kula da shi, Malam Yushau Shuaib, babban editan lakabin IMPR, ya nuna a wurin taron, Pantami ya yaba da shi a matsayin wani muhimmin kayan tarihi na al’adu da addini.

A nasa jawabin, Yusha’u Shu’aib ya bayyana godiyarsa ga Pantami da ya nuna farin cikinsa a bikin, ya kuma yaba da irin jajircewar tsohon ministan wajen bunkasa ilimi da ci gaban kasa.

Ya bayyana cewa an gina masallacin ne a cikin harabar cibiyar PRNigeria bayan aikin gina titi ya haifar da rushe wani masallaci da al’umma ke amfani da shi.

An kammala taron da addu’o’in samun ci gaban da al’umma baki daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here