NDLEA ta kama masu safarar miyagun ƙwayoyi, ta ƙwace hodar Iblis da kuɗin ta ya kai Naira Biliyan 5.3

WhatsApp Image 2025 09 07 at 10.28.05 750x430 (1)

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta bankaɗo wata ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi da ke aiki tsakanin Najeriya, Biritaniya, Brazil, Australia da Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ta kama shugabanni uku bayan gano hodar iblis da aka ɓoye cikin kayan dinki a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagos. 

Kwayar da aka kwace ta kai kimanin kilo 17.9, wadda darajarta a kasuwa ta kai Naira biliyan 5.3.

Bincike ya kai jami’an NDLEA ga kama wasu shugabannin ƙungiyar, ciki har da Muaezee Ademola Ogunbiyi da Shola Adegoke, inda a gidajensu an gano ƙarin kwayoyi, bindiga, da motoci.

Bincike ya nuna Ogunbiyi ya taba yin shekara 14 a gidan yari a Biritaniya kan kisan kai, yayin da Adegoke kuma ya taba zaman kurkuku a ƙasar Ingila kan safarar methamphetamine.

Babban jagoran ƙungiyar, Adebisi Ademola Omoyele, an ce yana boye a Dubai.

Karin karatu: NDLEA ta cafke mutum 6 bisa zargin saka kwaya a jakunkunan wasu yan Najeriya 3 da Saudiyya ta kama bayan zuwa umara

A wani samame daban a filin jirgin sama na Lagos, an kama wani ɗan Najeriya daga Italiya, Gabriel Michael, da magungunan Tramadol sama da 24,000, wanda ya yi niyyar safararsu zuwa Turai.

Haka kuma, a tashar jiragen ruwa ta Onne, Rivers, an gano kwalabe 160,200 na syrup mai codeine a cikin kwantena, da darajarsu ta kai sama da Naira biliyan 1.1.

Haka NDLEA ta ci gaba da kama wasu da dama a Abuja, Lagos, Kogi, Edo, Anambra da Niger, inda aka kwace daruruwan kilo na tabar wiwi (skunk, Loud da Colorado) da kuma tarin Tramadol.

A jihar Taraba kuma, an lalata gonakin tabar wiwi mai girman eka 7.5, inda aka kama manoman.

Hukumar ta ce wannan nasara na daga cikin ci gaba da yaki da safarar miyagun ƙwayoyi a fadin ƙasa, tare da wayar da kai ga al’umma karkashin shirin War Against Drug Abuse (WADA). An gudanar da wa’azi da ziyarce-ziyarcen fadakarwa a Nasarawa, Kano, Anambra da Kogi, domin rage yaduwar miyagun ƙwayoyi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here