A jawabinsa na farko tun bayan da aka fara zanga zangar nuna rashin amincewa da tsadar rayuwa a sassan kasar daban daban shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna takaici kan tarzomar da ta barke a wasu jihohin kasar.
Ya kuma ya nuna alhini a kan asarar rayukan da aka samu a jihohin Borno da Jigawa da kano da kaduna da kuma gine-ginen gwanatocci da dukiyoyin mutane da aka lalata da kuma sace-sace .
Game da haka ne shugaba Tinubu ya yi kira ga masu zanga zangar da su yi hakuri su dakatar da zanga zangar tare da bada damar zama kan teburin shawara.
”Na ji koken matasan kasarmu kuma kuma na cewa tsaddar rayuwa ce ta sa ku ka yi wannan zanga zangar” in ji shi
Ya ce gwamnatinsa a shirye take ta shawo kan matsalolin da suka kunno kai sakamakon matakan janyen tallafin man fetur da darajar naira da aka karya.
Shugaban kasar ya sake kare dalilan da suka sa gwamnatinsa ta dauki wadanann matakai yana mai cewa tattalin arzikin kasar na kan hanyar farfadowa kuma an samu raguwa a yawan kudaden da gwamnatin ke kashewa wajan biyan bashi daga kashi 97 cikin dari zuwa kashi 68 cikin dari a cikin watanni 13
Sai dai ya yi yi hanunka mai sanda ga masu amfani da zanga -zangar wajan tayar da zaune tsaye a kan cewa za a dauki mataki akansu.
Shugaba Tinubun ya yi yi kira ga jami’an tsaro da su ci gaba da aikinsu na kare rayuka da dukiyoyin mutane.
Ya kuma shaida wa ‘yan kasar cewa kada su bari rikici da barnata kayan al’umma su tahayyara kasar, kuma su yi aiki tare domin inganta makomar kasar.
Al’ummar Najeriya na fama da matsin tattalin arziki, musamman tun bayan da shugaban kasar ya sanar da cire tallafin man fetur a watan Mayun 2024.
Farashin kayan masarufi ya nunnunka sannan darajar kudin kasar ta yi zubewar da ba a tana gani ba a shekarun nan.
Wannan ne ya sa al’ummar kasar suka fara zanga-zangar kwana 10, daga ranar 1 ga watan Agusta.
Sai dai jawabin na shugaba Tinubu na ranar Lahadi, wanda aka yi tsammanin zai mayar da hankali wajen sanar da sabbin matakai na kawo sauki ga ‘yan kasa ya buge ne wajen zayyano shirye-shiryen da gwamnatinsa ta fito da su tun bayan kama mulki.
Matakan da mutane da dama a kasar ke ganin ba su yi wani tasirin a zo a gani ba wajen saukaka tsadar rayuwar da al’ummar kasar ke ciki.
Sannan jawabin bai ce komai kan matsalar tsaro da ke addabar wasu yankunan kasar ba.
Rashin tsaro, musamman a arewacin kasar na daga cikin dalilan da matasa suka kafa na gudanar da zanga-zangar.
Ko a cikin makon da ya gabata, an kai wani harin kunar bakin wake a jihar Borno, wanda hukumomi suka ce ya kashe mutum 16.
Shi ne hari na biyu a cikin wata biyu da ake zargin kungiyar Boko Haram da kaiwa, bayan wanda ta kai a garin Gwoza na jihar ta Borno, inda aka ruwaito cewa sama da mutum 30 ne suka mutu.
A arewa maso yammacin kasar ‘yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare suna kisa da kuma garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.