Matatar Man Fetir Ta Fatakwal Za Ta Dawo Aiki Disamba – Tinubu

Tinubu speaking 1 (1)

Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa shugabannin kungiyar kwadago cewa matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki nan da watan Disamba 2023.

Kungiyar kwadagon ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Laraba, a Abuja bayan wata ganawa da suka yi da shugaba Bola Tinubu.

Shugabannin kwadagon sun kuma bayyana cewa, shugaban ya yi alkawura da dama inda suka amince da komawa kan teburin tattaunawa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya, Joe Ajaero dana TUC, Festus Osifo suka fitar.

Sanarwar ta kuma yabawa ‘yan Najeriya bisa goyon bayan zanga-zangar da aka yi a fadin kasar.

“Haɗin gwiwar ya yi amfani sosai, an samu gagarumin sauyi da ta shafi al’amuran da suka dabaibaye ayyukan kwamitin shugaban ƙasa kan cire tallafin da ya sa aka yi zanga-zanga.

“Ya yi alƙawarin buɗe taswirar hanya mai aiki zuwa madadin CNG mako mai zuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here