Mambobin Majalisar Wakilai sun gudanar da wani taro na musamman a ranar Laraba inda suka gabatar da muhimman shawarwari kan gyaran tsarin aikin soji, tsarin shari’a, tsarin daukar ma’aikata da kuma dangantaka da al’umma domin magance karuwar matsalolin tsaro a ƙasar.
Taron ya mayar da hankali kan bukatar sabunta tsarin tsaro tare da inganta hanyoyin aiki a fannonin gwamnati daban-daban.
Tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar, Idris Wase daga jam’iyyar APC mai wakiltar Jihar Filato, ya bayyana cewa babban kaso na matsalolin tsaro a yammacin Afirka na faruwa a Najeriya.
Wase ya jaddada cewa dole a dauki matsalar tsaro a matsayin laifuka kai tsaye, ba tare da danganta ta da kisan kare dangi ko wani bangare na addini ko kabilanci ba.
Ya kuma nemi a sake duba tsarin tsaro gaba ɗaya domin tabbatar da ingantaccen tsari.
Wase ya yi nuni da cewa akwai bukatar a tsaurara tsarin daukar ma’aikata a hukumomin tsaro saboda rashin tsaftar tsarin yanq baiwa miyagu damar shiga.
Ya bukaci ’yan siyasa da ke bada shawarar daukar mutane su tabbatar da mutanen da ake ba da shawara kansu don ganin sun cika ka’idojin da ake bukata.
Ya kuma ce dole ne a gano wadanda ke lalata ayyuka a cikin rundunonin tsaro domin tsaftace tsarin.
Dan majalisa Sada Soli daga APC mai wakiltar Jihar Katsina ya jaddada bukatar hada kai da al’ummomi wajen shiryawa da aiwatar da dabarun yaki da rashin tsaro.
Soli ya ce al’umma su ne ke fuskantar wadannan laifuka kai tsaye, don haka dole ne su taka muhimmiyar rawa wajen samar da tsaro.
Aliyu Betara daga APC na Jihar Borno ya bukaci a sake fasalin yadda ake ware kudaden tsaro, yana mai cewa kayan aikin soji suna daukar lokaci mai tsawo kafin a samu, don haka zuba jari a manyan kayayyaki zai taimaka wajen gaggauta ayyukan rundunonin tsaro.
Ibrahim Isiaka daga APC mai wakiltar Jihar Ondo ya bayyana cewa gwamnati da hukumomin tsaro suna kokari, amma akwai bukatar kara karfafa dangantaka da kasashe makwabta domin dakile laifuka da ke ketare iyakoki.
Enwo Igariwey daga PDP na Jihar Ebonyi ya bayyana cewa matsalar tsaro an sha tattaunawa akanta tare da bayar da shawarwari, amma matsalar ita ce rashin aiwatar da shawarwarin da aka tsara.
A nasa bangaren, Solomon Bob daga PDP mai wakiltar Jihar Rivers ya soki yadda ake sasanta da ’yan ta’adda maimakon aiwatar da hukunci bisa doka.
Ya ce idan ana ceto wadanda aka yi garkuwa da su, masu laifin kuma ba su fuskantar hukunci, hakan ba ya taimakawa tsarin yaki da ta’addanci.
Ya nemi gaggauta dakatar da tattaunawa da ’yan ta’adda tare da kama wadanda ke kare su a bainar jama’a.
NAN













































