Kotu ta tasa keyar Danbilki Kwamanda zuwa Gidan Yari

dan bilki, kotu, gidan yari
A ranar Talata ne wata kotun majistare da ke zamanta a Jihar Kano ta tasa keyar fitaccen mai sharhi akan harkokin siyasa, Abdulmajid Danbilki Kwamanda zuwa...

A ranar Talata ne wata kotun majistare da ke zamanta a Jihar Kano ta tasa keyar fitaccen mai sharhi akan harkokin siyasa, Abdulmajid Danbilki Kwamanda zuwa gidan gyaran hali.

Bayan shiga kotun, a karshe kotun ta dage zamanta zuwa ranar Litinin, 29 ga watan Janairu domin sake zama.

Karanta wannan: Badakalar Naira Biliyan 4: Tsohon Gwamnan Anambra Obiano ya isa Kotu

SOLACEBASE ta rawaito cewa Danbilki Kwamanda, ana tuhumarsa ne da laifin kalaman tunzuri da ka iya jawo rashin zaman lafiya ga al’ummar Kano da dai sauransu.

An bayyana cewa an kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kuliya saboda kalaman bata suna da suka shafi Masarautar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here