Jam’iyyar PDP da ta ADC sun yi Allah wadai da harin da aka kai makarantar gwamnati ta ’yan mata da ke Maga a ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi, wanda ya haifar da kashe mataimakin shugaban makarantar Malam Hassan Makuku da sace ɗalibai mata da dama.
’Yan bindigar sun kai farmakin ne da daddare, inda suka kashe mataimakin shugaban makarantar sannan suka tafi da wasu ɗalibai mata, lamarin da ya sa jami’an tsaro na ’yan sanda da sojoji da masu sa kai ke bazama a dazuzzuka domin ceto su lafiya.
A cikin sanarwar PDP, sakataren yaɗa labarai na ƙasa Ini Ememobong ya bayyana cewa wannan kisa da sace-sacen wani abin bakin ciki ne da ya zame wa al’umma a zamanin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, yana mai hasashen cewa tabarbarewar tsaro ta yi tsanani a faɗin ƙasar nan.
PDP ta kuma ce gwamnatin jam’iyyar APC ta gaza kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan mamacin da iyayen ɗaliban da aka sace, tana kira ga shugaban ƙasa da ya ɗauki mataki mai ƙarfi domin kare rayukan jama’a ba tare da dogaro da waje ba.
Sanarwar ta ƙara nuna cewa faruwar lamarin na Maga ya zo ne a lokacin da aka ruwaito karuwae sace-sace a Nasarawa da Filato da Kano da Katsina, tana mai cewa wannan al’amari ya saba wa bege da fatun da ’yan ƙasa suka yi na samun ingantaccen tsaro.
A nasa bangaren, sakataren yaɗa labarai naJam’iyyar ADC Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa wannan hari ya ƙara tabbatar da tabarbarewar tsaro a ƙasar, yana mai cewa an sha yi wa gwamnati gargadi ta tunkari matsalar da gaggawa amma ta yi kunnen uwar shegu.
Ya ce, sace ɗaliban bai kamata ya sake zama irin abin da ya faru da matan Chibok ba, yana kira ga shugaban ƙasa da ya tabbatar an ceto su ba tare da ɓata lokaci ba kana ya buƙaci hukumomin tsaro su yi aiki cikin gaggawa, ƙwarewa da haɗin kai domin kawo ƙarshen lamarin.













































