Iyalin amarya sun bayyana dalilin sauya wurin daurin auren dan Barau Jibrin zuwa Abuja

Barau JIBRIN SABO 600x430

Iyalin Maryam Nasir Ado Bayero, ‘yar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, sun bayyana dalilin da ya sa aka sauya wurin daurin aurenta da Jibrin Barau Jibrin, ɗan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, daga Kano zuwa Abuja.

A wata sanarwa da Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Dan Agundi, ya fitar, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin shirye-shiryen auren, ya musanta jita-jitar da ke cewa an sauya wurin ne saboda matsalolin siyasa da suka shafi Dokar Gyaran Haraji.

Ya bayyana cewa bisa al’ada, iyayen amarya ne kawai suke da hakkin zaɓar wurin daurin aure, kuma sun zaɓi Abuja ne tun makonni da suka wuce domin sauƙaƙa wa baƙi daga cikin gida da waje su samu damar halarta.

Dan Agundi ya yi kira ga jama’a da su daina siyasantar da wannan aure, yana mai cewa aure ibada ne mai tsarki, ba kuma ya kamata a danganta shi da batutuwan siyasa ba.

An shirya gudanar da daurin auren ranar Juma’a, 13 ga Disamba, 2024, a Abuja.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here