Hukumar kula da shige da fice ta ƙasa za ta ƙaddamar da Fasfo na gaggawa ga ‘yan Najeriya da ke ƙasashen waje

Passport new 750x430

Hukumar kula da shige da fice ta ƙasa ta sanar da shirin ƙaddamar da sabon Fasfo na gaggawa guda ɗaya da ake kira Single Travel Emergency Passport (STEP) domin ƙarfafa tsarin tantance shaidar ‘yan ƙasa da inganta tsaron iyakoki bisa ƙa’idojin duniya.

Babban kwamandan hukumar, Kemi Nandap, ta bayyana hakan a taron haɗin gwiwa na Khartoum, Rabat da Niamey Processes wanda Najeriya da gwamnatin ƙasar Faransa suka jagoranta.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Akinsola Akinlabi, ya fitar a ranar Laraba a Abuja, Nandap ta ce sabuwar takardar tafiyar za ta maye gurbin tsohuwar Emergency Travel Certificate (ETC) da ake amfani da ita a yanzu.

Ta bayyana cewa STEP za ta zama takardar tafiya ta wucin gadi guda ɗaya ga ‘yan Najeriya da ke ƙasashen waje waɗanda fasfotinsu ya ƙare, ya ɓace ko aka sace musu, domin ba su damar komawa gida cikin tsari mai aminci da sahihanci.

Nandap ta ce za a rika bayar da wannan fasfo ne a manyan ofisoshin jakadancin Najeriya da ofisoshin jakadanci na ƙasashen waje, kuma wannan shiri na daga cikin muhimman gyare-gyaren hukumar don sauƙaƙa ayyukan hijira da inganta hidimar jama’a.

Haka kuma ta bayyana cewa wannan mataki yana cikin tsarin hukumar na tabbatar da tsaron bayanan ‘yan ƙasa, ingantaccen tallafin ofisoshin jakadanci da kuma ƙarfin kula da iyakoki.

Ta ƙara da cewa hukumar na ɗaukar matakai wajen ƙarfafa tsare-tsaren kula da iyakoki, inganta tsarin gudanar da hijira, horar da ma’aikata da kuma ƙara haɗin gwiwa da ƙasashen duniya domin yaƙar safarar mutane da ta’ammali da ‘yan gudun hijira.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa taron ya haɗa da muhimman masu ruwa da tsaki a fannin hijira ciki har da hukumar kula da ‘yan gudun hijira, masu hijira da waɗanda rikici ya raba da muhallansu (NCFRMI), hukumar hana safarar mutane (NAPTIP), ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma (ECOWAS), ƙungiyar tarayyar Afirka (AU), ƙungiyar Tarayyar Turai (EU), da sauran ƙasashen Afirka da Turai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here