Gwamnatin Tarayya ta zargi masu yaɗa manufofin ƙasashen waje da tallafawa wajen zuzuta zargin kisan kiyashi ga Kiristoci da Amurka ta yi

Minister of Information and National Orientation Mohammed Idris 720x430

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa wasu masu yaɗa manufofin ƙasashen waje, musamman na Amurka, ne ke taimakawa wajen yada labaran da ke nuna cewa ana kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya, abin da ya rinjayi yadda ake kallon matsalolin tsaro na ƙasar a duniya.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, inda ya ce binciken gwamnati ya gano cewa ana ƙoƙarin karkatar da gaskiya game da halin tsaro a Najeriya.

Idris ya ce gwamnati ta gano alaƙa tsakanin wasu masu yada manufofi na ƙasashen waje, musamman daga Amurka, da kuma wasu mutane a cikin ƙasar da ke da hannu a aikata laifuka.

Ya ce waɗannan alaƙa na nuni da cewa akwai hannun wasu daga waje, wajen yada labaran ƙarya kan halin tsaro.

Wannan furuci na zuwa ne bayan da gwamnatin Amurka ta sake sanya Najeriya cikin jerin “ƙasashen da suke da damuwa ta musamman” bisa zargin tauye ‘yancin addini da kuma kisan Kiristoci, abin da gwamnatin Najeriya ta ƙi amincewa da shi.

Ministan ya jaddada cewa duk da matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar, babu wata shaida da ke nuna cewa ana kai hare-hare bisa bambancin addini, domin Musulmi da Kiristoci dukkansu na fuskantar barazana iri ɗaya.

Ya ce matsayin da Amurka ta ɗauka ya samo asali ne daga bayanan ƙarya da aka yaɗa, yana mai cewa ƙungiyoyin ta’addanci a Najeriya ba sa aiki bisa layin addini.

Idris ya kuma bayyana cewa dakarun tsaro a ƙarƙashin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 13,500, sun kama fiye da 17,000, tare da kubutar da mutane sama da 9,850 da aka sace tun daga watan Mayu 2023.

Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da yin aiki tare da ƙasashen duniya domin kawo ƙarshen ta’addanci da tabbatar da tsaro a fadin ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here