Da ɗumi-ɗumi: Ganduje ya kada tsagin Shekarau a kotun ƙoli

Ganduja Smiling
Ganduja Smiling

A yau Juma’a ne kotun ƙolin Najeriya ta yi watsi da ƙarar da ɓangaren Malam Ibrahim Shekarau na jam’iyyar APC suka shigar a kan tsagin gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar a Kano.

Kotun ƙolin ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara wadda ta bai wa ɓangaren Ganduje shugabancin jam’iyyar APC a Kano inda ta tabbatar da zaɓen da ɓangaren gwamnan suka gudanar.

A hukuncin da kotun kolin mai alƙalai biyar ta yanke wanda mai shari’a Ibrahim Saulawa ya sanar, kotun ta ce, babbar kotun birnin tarayya Abuja ba ta da hurumin yin shari’ar a matakin farko.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here