Yadda Gwamnatin jihar Kano ta magance matsalar rashin tsaro a makarantu gwamnati

Kano Map
Kano Map

“A bayyane yake halin da makarantun gwamnti suke ciki a wasu shekaru a baya ta fuskar barazanar rashin tsaro daga bata-garin da suke maida makarantun guraren da suke cin karensu babu babbaka.

saboda fahimtar da s ka yi cewa babu mai iya tanka musu.

Idan ma suka ga dama basa fita daga makarantun har sai lokacin da suka ga damar fita sannan mu Kuma mu share namu faggen na koyawa yara ilmi.

” Kuma ba wani abune ya haifar da hakan ba illa rashin katange makarantun fomin basu tsaron da ya dace.

” Kafin zuwan tsarin karkashin gwamnati mai ci a halin yanzu , makarantu sun fuskanci kakubale musamman makarantun cikin kwayar birni da kewaye.
“Inji daya daga cikin shuwagabannin makarantun sakandiren da matsalar ta shafa.

Manyan kalubalolin da makarantun gwamnti suka fi fuskanta abangaran ilmi musamman a wadancan lokuta da suka shude sune batun rashin cikakken tsaro a makarantun gwamnati ta yanda binkice ya tabbatar da cewa wasu daga cikin makarantun sun tasamma zama matattaran aikata manyan laifuka a lokacin. Tun daga kan fatauci da sha da sayarda da miyagun kwayoyi da Kuma uwa uba boye makaman da ake fita ayi ta’adanci dasu.

Galibin irin wadanda abubuwa kan faru har a lokutan da dalibai ke haramar shiga ajujuwa domin daukar karatu inda a Kan yi rashin sa’ar iske irin wadancan bata gari suna kokarin fitowa daga ajujuwa yayin da wasu ke dirowa daga rufin dakunan ajujuwan domin fita ayyukansu na ta’adanci.

Wadannan mugwayen halaye da dabiu su suka jawo ra’ayin wasu daga cikin iyayen na cire yayansu kaco-Kan daga makarantun gwamnati saboda fargabar abubuwan dakanje su zo.

Ta yanda lamarin kai tsaye ya ke shafar ilmi wasu daga cikin daliban da iyayensu ke daukar wancan mataki Maza da Mata baya ga daliban dake kokarin shiga babbar makarantar sakandire wadanda suma lamarin ke shafa.

Binkice da jaridar solace base ta gudnar ya nuna cewa makarantun da ke fuskantar wadannan kalubale sun hada da babbar makarantar sakandiren gwamnati ta Stadium dake titin Airport da sakandy Yan mata ta Dabo dake Kan titin France Road, da sakandiren Yan Mata ta Kwachiri da ta Chiranci da sauran makarantun dake yankin cikin Birnin Kano

Saidai a dai-dai lokacin da lamarin yayi karfin da yake nema yafi karfin kowa kwatsam’ sai gwamnatin Kano tayi wani karatun ta nutsu’ ta hanyar bullo da wani shirin hadin guywa da wasu bangarori masu zaman kansu ta yanda zaa Samar wa wadancan makarantu mafita daga halin da suka tsinci kansu na rashin cikakken tsaro.

“An bujuro da shirin ne karkashin shawarwari da bukatun neman yin hakan daga bangaran makarantu da suka fi fuskantar matsaloli rashin tsaro saboda bata-garin da suka addabesu da shaye shaye da sauran laifuka”
Kamar da yanda wasu daga cikin jami’an kula da tsaren tsaren gyaran makarantun gwamnatin jihar Kano suka bayyana.

Shirin hadin guywa tsakanin gwamntin da bangarori masu zaman kansu da aka yiwa lakabi da (PPP ) shirine da gwamnatin Kano tace ta samar dashi ne domin Samar da ishashen tsaro ga makarantun gwamnati tare basu kulawa ta musamman abangaran gudanarwa da Kuma cimma nasarar shirin gwamnatin Kano na ilmi kyauta.

An kuma dora alhakin kula da shirin ga wasu bangarorin gwamnati domin aywatar dashi.

Bangarorin kuwa sun Hadar da hukumar raya Birane ta jihar Kano (KNUPDA) da Majalisar Dokoki ta Jiha, da Kwamitin Gudanar da Makarantu na jihar Kano (SBMC) da kuma Kungiyar Iyaye da Malamai (PTA)

Tuni dai Masana lamuran yau da kullum ke kallan tsarin a matsayin hanyar da zata taimaka wajen magance kalubalen da ke tattare da karancin koyo da koyarwa a makarantu harma da mangance barazanar rashin tsaron da makarantun ke fuskanta.

Sai dai wasu daga cikin masu tsokaci Kan lamuran yau da kullum suna kallan lamarin a matsayin nakasu a bangaran kwazan dalibai musamman duba da cewa galibin makarantun da tsarin zai shafa makarantu da za’a gine su da shaguna wanda haka na iya shafar harkokin karatu a gaba’ saboda matse makarantu da za’a rikayi da shaguna a lokuta daban daban.

Saidai cikin martanin da ya mayar Shugaban hukumar tsara Birane ta jihar Kano KNUPDA, Arch. Sulaiman Ahmed Abdulwahab, Ya ce “Haryanzu Alumma da dama basu gama fahimtar Alkhairan da shirin zai haifar ga cigaban ilmi a jihar Kano ba.

Yace ayyukan kewaye wasu daga cikin makarantun da suke fuskantar matsalar tsaro ayyukane dake gudana karkashin wannan shiri ta yanda makarantun zasu samu cikakken tsaro, saboda shagunan dake kewaye dasu, baya ga samun cikakkiyar kulawa a bangaran gudanarda danar gudanar da makarantun yanda ya kamata

” A yanzu haka ma maganar da ake tuni muka cimma matsayar fara gudanar da ayyukan gyaran wasu daga cikin makarantu gwamnatin Kano karkashin wannan shiri na PPP wanda domin shirine na hadin guywa da wasu bangarori masu zaman kansu domin samun hanyoyin kula da makarantu da basu tsaro da isassun kudaden gudanar dasu” fara ayyukan gyaran wasu daga cikin makarantun”

” Munyi nasarar tantance makarantu guda 21 mallakin gwamnatin jihar Kano wadanda zamu fara wannan aiki.

” Saidai dukkanin abubuwan da muke fatan cimma nasara zasu tabbatane gwargwadan hadin guywa da goyan bayan jama’a.

Saboda haka muna rokon Al-umma su fahimci shirin sosai saboda muhimmancinsa wajen inganta shaanin ilmi” inji MD KNUPDA.

Arch Suleiman Ahmad ya kara da cewaa ” A yanzu haka ma hukuma tana nazarin neman hadin guywar majalisar dokokin Kano Kan gyaran dokar kula da lamuran da suka shafi abubuwan da ake gudanarwa na sanaa a kewayen makarantu ta yanda gwamnati za ta samu hurumi sosai a bangaran yanda gudanar da lamura a kewayen makarantu.

A ziyarar baya bayan nan da ya kai wasu daga cikin makarantun da lamarin ya fi shafa,shugaban hukumar tsara Birane ta jihar Kano Arch Suleiman Ahmad ya bayyana cewa sama da kashi 85% na ayyukan gyaran makarantun guda takwas’ kashi na farko ya kammala, da suka hada da babbar makarantar sakandiren G.S.S, Stadium da makarantar sakandiren Mata ta G.G.S.S.S Dabo,da babbar makarantar sakandiren G.S.S Kwakwachi da babbanr sakandiren Bachirawa, da sakandiren Kofar Nasarawa, da sakandiren Yan mata dake Dukawuya, da sakandiren Goron Dutse, da sakandiren yan Mata ta Chiranchi da kuma makarantar primary daje Chiranci.

Shugaban kwamitin gudanar da makarantun ( SBMC ) na makantar sakandiren gwamnati ta Stadium Alhaji Muhammad Lawal, ya ce sun kwashe sama da shekaru shida suna rubuta koke-koke ga gwamnatin jihar Kano kan lalacewar kayayyakin koyo da koyarwa da matsalar rashin tsaro da ta addabi makarantar.

“Mun dade muna cikin wannan hali kafin zuwan wannan shiri na kula da makarantu gashi a yanzu ga shi a yanzu shirin ya taimaka wajen katange mana makaranta da gina karin sabbin Ajujuwa bakwai ( 7) da bandakuna goma sha biyar (15) da Kuma gyara dakunan gwajegwajen makarantar ” Inji Muhammad.

Haka lamarin yake a bangaran makarantar sakandiren Yan mata ta Dabo dake kan titin France Road) Kano, shugabar makarantar Hajiya Binta Abdul Hamid, ta ce babban kalubalen da ya addabi makarantar a wancan lokaci shine batun barazanar tsaro daga masu shaye-shayen dake haurowa makarantar daga unguwar Sabongari saboda kusancin makarantar da Unguwar.

“Gaskiya tunda makarantar ba ta da katanga, hakan ya sa ’yan bata-gari su ke haurowa makarantar cikin sauki tare da sace kayayyakin makarantar batan sun yi shaye shaye a makarantar.

” Don haka suke samun damar haurowa su saci kayan makarantar yi sata da lalata mana dukiya. Wani lokaci sukan shiga ofis ta silin su aikata barna da ta’adanci.

Saboda haka a shekarar 2015 muka yi taron hadin gwiwa na PTA na makarantu a Sabon Gari tare da mika kokenmu ga gwamna” Inji Hajiya Binta.

Hajiya Binta ta kara da cewaa “Mun ba da shawarar gina shaguna a katangun makarantun da suke da irin wannan matsala, saboda samar da shagunan zai Samar da tsaro saboda masu shagunan za su hada kai da jami’an tsaro domin kare dukiyoyinsu.

Tabbas wannan shiri ya taimaka wajen ragewa gwamnati nauye- nauye.
Domin kuwa mun gina katangu guda biyu , da bandakuna goma (10) da sauran gyare gyaren makaranta.

Shima Shugaban makarantar sakandire gwamnti ta G.S.S Kwakwachi, Malam Auwalu Ado, ya ce makarantar da aka kafa a shekarar 1983 ba a taba ganin wani gyara da ya kai ga rushewar gine-gine da rufin ajujuwa ba.

Ya ce katangar makarantar ta dade da lalacewa saboda yawan ambaliyar da rafin dake gefen makarantar ke yawan yi.

“Rushewar katangar ya sa mu fuskantar muminar barazanar tsaro daga Yan daba da masu shaye shaye wadanda galibi suka mamaye makarantar domin sace rufin rufin kwano da tagogi da kofofi da sauran kayayyakin makaranta.” in ji shi.

Ado ya ce “Mun mika rubutacciyar makarantar kwamitin SBMC da PTA da kuma gudanarwa sun fara rubuta wasikun korafe-korafe tun a shekarar 2007 tare da yin kira da a gyara. Kafin daga baya su tuntubi hukumar tsara Birane ta jihar Kano KNUPDA kan halin da makarantar ke ciki Inda abin mamaki a halin yanzu hukumar na gudanar da aikin gyaran makarantar ka-in da na-in ”

Hakazalika, shugaban kwamitin gudanar da makarantu na babbar sakadiren gwamnti ta G.S.S Kofar Nasarawa, Malam Habibu Dauda Yakasai, a lokacin da yake yabawa shirin ya ce abun a yaba wa hukumar tsara Birane ta jihar Kano KNUPDA ne saboda ta gyara ajujuwa guda shida a makarantar, ta gina bandakunan dalibai shida da bandakunan ma’aikata biyu don magance matsalar karancin ajujuwa da Kuma kauda matsalar tsuguno a guraren da basu dace ba.

A nasa bangaren, daraktan tsara gine-gine na hukumar KNUPDA, wanda shine shugaban kwamitin na jihar Kano , Arch. Salisu Bello, ya ce an cimma kusan kashi 90 cikin 100 a matakin farko aikin gyaran makarantun da suke da manyan matsaloli.

Yace makarantu goma sha biyu ne 12 wadanda ake saran kammala su a kashi na biyu na shirin.

Salisu ya ce ana gudanar da gyare-gyaren ne tare da amincewar hukumomin makarantun domin a tabbatar da cewa aikin da aka yi ya yi dai-dai da manufofin da aka tsara domin cigaban harkokin ilmi a jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here