Peter Obi ya fidda kundin manufofin sa me shafi 72

Peter Obi
Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi ya fitar da kundin manufofin yakin neman zabensa.

Rahotanni sun ce kundin mai shafi 72, da ya kunshi hasashe da rashin jituwa tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar LP da jam’iyyun adawa da sauran masu ruwa da tsaki.

Rahoton yace kundin manufofin Dan takarar, an fitar da shine a shafin sa na Twitter da aka tabbatar a safiyar Lahadi ta karshen mako.

Obi ya rubuta, “Ina farin cikin gabatar da kundin manufofin mu mai shafuka 72, mai take, ‘Abune Mai yiwuwa: Yarjejeniyar mu da ‘yan Najeriya.

A cikin bayanin, Peter Obi ya yi alkawarin fitar da Najeriya daga halin da tattalin arzikin kasa ke ciki, bunkasa amfanin gona dakuma samar da kayayyaki.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP ya ce zai kawo karshen ‘yan fashi da tayar da kayar baya idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

“Zamu habbaka manyan ababen more rayuwa don samar da ingantacciyar wutar lantarki, layin dogo, zirga-zirgar titi, da hanyoyin sadarwa ta hanyar hadin gwiwar jama’a da masu zaman kansu, da gudanar da harkokin kasuwanci na jama’a.

“Zamu kawo tsare tsare ga matasan Najeriya don haɓaka aiki Dan yi goggaya a duniya ta hanyar sanya hannun jari cikin manyan makarantu da bincike, ingantaccen kiwon lafiya, da ilimin kasuwanci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here