Fassarawa:Aminu Bala Madobi-Daga Kano
Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ta bukaci hukumar masu yiwa kasa hidima da ta shigo cikin shirinta na kasuwanci domin bunkasa shirin bunkasa sana’o’in hannu da habaka kasuwanci (SAED).
Shugaban Jami’ar Farfesa Kabiru Bala ne ya yi wannan kiran a lokacin da Jami’in hukumar na jihar Kaduna Mista Odoba Oche ya kai masa ziyara a zariya.
Bala wanda ya samu wakilcin babban mataimakin sa farfesa Ahmed-Doko Ibrahim yace ziyarar anyi ta ne danufin inganta alakar Jami’ar da hukumar masu yiwa kasa hidima.
Ya ce shirin hadin gwiwar zai bunkasa dabarun samar da ayyukan yi da kuma karfafa kwarewar da ake bukata wajen samar da ayyukan yi ga mambobin kungiyar da sauransu.
Tun da farko a tsokacin dayayi, Jamiin Shirin hukumar masu yiwa kasa hidima a Kaduna, Mista Oche ya bayyana Jami’ar ta ABU a matsayin abar alfahari wadda ke kyautata tsarin manhajar tun lokacin da aka fara shirin SAED a shekarar 1973.
Mista Oche ya bayyana cewa Jami’ar Ahmadu bello a koda yaushe na bada gudumawa wajen samun nasarar shirin yiwa matasa hidima na kasa.
Oche daganan yace Jami’ar Ahmadu bello babbar cibiya ce wacce ke ta cigaba da bunkasa kuma tayi fice a matakin koyo da koyarwa, bincike da hidimtawa al’umma.













































