Shugaban karamar hukumar Ungogo dake jihar Kano, ya shiga sahun matasan shugabanni 50 a Afrika musa tasiri a rayuwar al-umma

IMG 20220724 WA0247
IMG 20220724 WA0247

Shugaban karamar hukumar Ungogo, Abdullahi Garba Ramat, ya sami shaidar girmamawa a hadaddiyar Daular Larabawa ta Dubai, ya yin da suka bayyanashi a matsayin daya daga cikin matasan shugabanni 50 masu tasiri a Afrika.

Ramat ya shiga sahun matasan shuwagabani masu tasiri a Afrika ne bisa kokarin sa na samarwa da matasa aikin yi, samar da tsaro a yankin sa, da kuma gudunmawar da yake bayar wa wajin bunkasa fasahar zamani.

Maimartaba Sheikh Rashid bin Majid Al Mualla, wanda shine shugaban hadaddiyar Daular Larabawa ta Dubai, ne ya bada shaidar girmamawar, wanda ya sami wakilcin yarima Ebrahim Sanyang, wajan bada shaidar.

Yayin bada shaidar, yariman ya ce an bada shaidar girmamawar ne domin zaburar da matasan shugabanni a nahiyar Afrika wajan cigaba da bawa bil’adama gudunwa ta kowa ce fuska da kuma zama jagoruri na gari ya yin gudanar da shugaban cin su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here