Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta amince da kafa sabbin Masarautu a Jihar

Matawalle
Matawalle

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta amince da kafa wasu Karin masarautu biyu a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran majalisar Nasiru Biyabiki ya fitar ranar Juma’a a Gusau babban Birnin Jihar.

Sanarwar tace amincewar ta biyo bayan gyaran dokar kafa masarautun jihar mai lamba 15 ta shekarar 2000, domin baiwa jihar damar samar da karin masarautu.

“Majalisar ta amince ne a zamanta na ranar juma’a, kuma masaurautun biyun da za a kara sun hadar da Masarautar Yandoton Daji da kuma masarautar Bazai”. Inji Biyabiki.

A cewarsa Yandoton Daji it ace za ta kasance masarauta mai daraja ta biyu, data kunshi gundumomin ‘Yandoton Daji da Keta da Kizara da Bawa-Ganga da Kwaren-Ganuwa sai Danjibga da kuma Kunchin-Kalgo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here