Yanzu-Yanzu: Sarkin Gumel, Alhaji Ahmed Sani ya rasu

Emir of Gumel 750x430

Sarkin Gumel a Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Muhammad Sani na II, ya rasu.

Majiyoyi daga fadar Sarki sun bayyana cewa ya rasu a Cairo ta kasar Masar a ranar Alhamis, inda ya yi jinya da karbar magani.

An haifi marigayin a ranar 12 ga Disamba, 1942.

Marigayi Sarkin Gumel na 16 ya rasu yana da shekaru 83, inda yake dab da cika shekaru 84.

Yana daya daga cikin sarakunan gargajiya da suka fi dadewa kuma suka fi daraja a Arewacin Najeriya.

Ya hau gadon sarauta a ranar 16 ga Disamba, 1980, bayan rasuwar mahaifinsa, an ba shi sanda da takardar sarauta a watan Mayu 1981.

Ya yi mulki sama da shekaru 45.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here