Masarautar Kano ta karyata jita-jitar da ke yawo cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya gaza cika sharuddan karatunsa na digirin lauya.
Wani bidiyo dake yawo a dandalin sada zumunta tun a ranar Lahadi, wanda ke zargin cewa Sarki Sanusi ya fadi wani kwas a cikin darusansa.
Sarki Sanusi ya yi rajista a matsayin dalibi a shekaru ta biyu a tsarin digiri na farko a fannin Shari’ar Musulunci da Dokokin Bai-daya a Jami’ar Northwest da ke Kano.
Babban sakatare a ofishin Sarki, Muhammad Ado, ya bayyana cewa bisa bayanan da suke da su, maki guda daya kacal ya rage wa Sarkin don ya kai matakin daraja ta daya (First Class).
“Mun halarci wani taro da daliban fannin lauya na jami’ar suka shirya a ranar Asabar, kuma wani dalibi ne ya dauki wannan bidiyon, amma maganar ba gaskiya ba ce.
“A lissafinmu, maki daya kacal ya rage wa Sarki ya sami First Class.
“Sunday Dare be ya kasance babban bako mai gabatarwa a wajen taron,” in ji Ado.
Wani dalibi a jami’ar mai suna Ibrahim Abubakar-Danmasani, ya bayyana cewa har yanzu ba a fara jarrabawa a makarantar ba, inda ya kara da cewa ana sa ran fara jarrabawar ce a ranar Litinin.
Wasu majiyoyi a makarantar sun tabbatar da kalaman Masarautar, inda suka bayyana cewa bidiyon da ke yawo ba gaskiya ba ne.
Majiyoyin sun yi ikirarin cewa wasu matasa ne suka yi bidiyon don nuna barna da son zuciya. (NAN)












































