Majalisar Wakilai ta fara binciken Jami’an Tsaron Ma’adanai kan zargin Naira biliyan 2

Reps Reps

Majalisar Wakilai ta yanke shawarar gudanar da bincike kan ayyukan Hukumar Jami’an Tsaron Hakon Ma’adanai, wacce ta kunshi jami’ai fiye da 2,200 da aka dauko daga Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC).

Wannan kudurin ya biyo bayan amincewa da wani kuduri da Hon. Abdulmaleek Danga, Dan Majalisar APC daga Kogi ya gabatar a zaman majalisar a ranar Laraba.

Danga ya bayyana cewa Ma’aikatun Tarayya na Ci Gaban Ma’adanai da na Harkokin Cikin Gida ne suka kaddamar da wannan dakarun tsaro na musamman a ranar 21 ga watan Maris 2024.

Ya ce an kafa rukunin ne bisa dashi na 3 na Dokar NSCDC da tsarin mulkin dokar Ma’adanai da Hako Ma’adinai ta Kasa ta shekarar 2007.

A cewarsa, an kafa jami’an tsaron ne domin kare wuraren hakar ma’adanai, yaki da haramtaccen hako ma’adinai da ‘yan fashi a garuruwan da ke da arzikin ma’adinai da kuma kare kudaden shiga na gwamnati daga bangaren ma’adanai.

Sabanin haka, dan majalisar ya yi zargin cewa sashin ya kauce wa humurninsa, wanda hakan ya yi sanadiyyar kama mutane ba bisa ka’ida ba da kuma tsangwama ga halaccin masu rike da lasisin hakar ma’adanai.

Ya kuma yi zargin sashin da rashin gaskiya a harkokin kudi, inda ya ce an gano sama da Naira biliyan 2 a asusun banki na tsohon kwamandan jihar.

Danga ya ce an sake tura kwamandan zuwa wani wuri maimakon a gurfanar da shi ko a gudanar da binciken shari’a ko ladabtarwa a cikin hukumar, wannan ne ya kara karfafa zargin cewa kungiyoyin masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba masu kudi sun saye a sashen.

Ya kuma nuna damuwarsa kan siye da rabon motoci na aiki ba tare da wata tabbatacciyar hujja ta amincewar majalisa ko tanadi a kasafin kudi ba.

Majalisar ta ba Kwamitinta kan Ci Gaban Ma’adanai umarnin gudanar da cikakken bincike kan ayyuka da sakamakon jami’in tsaron a fadin kasar.

Yayin da yake yanke hukunci kan hanzarin, Mataimakin Shugaban Majalisa, Benjamin Kalu ya umarci kwamitin da ya mika rahotonsa nan da makonni huɗu domin ɗaukar matakin majalisa na gaba. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here