Hukumar Hisbah ta Jihar Kano za ta fara yin gwajin lafiya ga ma’aurata 3000 da zata aurar a shirin auren gata na gwamnati jihar a ranar Litinin.
Mataimakin Kwamanda Janar na Hukumar, Mujahideen Aminudddeen ne ya sanar da hakan a ranar Lahadi, inda yace dole ne ma’auratan da za su yi aure daga kananan hukumomi 24 su je ofisoshin hukumar Hisbah na yankinsu ranar Litinin domin yin gwajin.
A cewar Aminudddeen, kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Rogo, Wudil, Tudun Wada, Warawa, Kibiya, Dawakin Tofa, Garun Malam, Kura, Dambatta, Karaye, Tsanyawa, Minjibir, Rimin Gado, Shanono, Kabo, Tofa, Rano, Bebeji, Ajingi, Gwarzo, Sumaila, Kiru, Takai, da Madobi.
Ya ce gwajin zai hada da gwajin HIV/AIDS, hepatitis, dacewar jini (genotype), ta’ammali da miyagun kwayoyi, da gwajin ciki ga mata.
Mataimakin Kwamanda Janar na Hisbah ya jaddada cewa wadanda kawai za su wuce gwajin ne za a ba su damar shiga shirin auren jama’a.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana kudirin da ya gabata na daukar nauyin auren maza 1,500 da mata 1,500, galibi gwauraye, mata da aka saki, marayu da masu karamin karfi.
Kowane ango zai samu Naira 100,000 a matsayin tallafin sadaki, yayin da za a ba ma’auratan kayayyakin gida irin su katifu, kayan sakawa da abinci.
Bugu da kari, masu cin gajiyar za su samu tallafin Naira 100,000 domin fara kananan sana’o’i.
Shirin, wanda Hukumar Hisbah ta shirya, na da nufin inganta zaman lafiyar al’umma, rage radadin tattalin arziki, da kuma karfafa iyalai a fadin jihar.












































