Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana goyon bayansa ga neman sake tsayawa takaarr dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Bichi, Hon. Abubakar Kabir Abubakar (Abba Bichi), gabanin zaben 2027.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Gwamnan ya bayyana hakan a lokacin taron tabbatar da takarar dan majalisar a APC da aka gudanar a Bichi, inda Abba Bichin ya zama dan takara daya tilo na jam’iyyar a kujerar Majalisar Wakilai.
Gwamna Yusuf ya yaba wa dan majalisar bisa abin da ya kira wakilci mai inganci da ayyukan yankin da ke da tasiri a fadin karamar hukumar ta Bichi.
“Ina so in yaba wa Hon. Abubakar Kabir Abubakar bisa wakilci mai inganci.
“Daga shekarar 2023, na kasance ina addu’a ga Allah Madaukaki da ya ba ni damar yin aiki tare da shi, kuma yau muna aiki tare domin ci gaban Bichi da Jihar Kano,” in ji gwamnan.
Ya bayyana cewa kokarin Abba Bichi na karfafa matasa da cigaban al’umma ya ci gaba da kawo sauyi mai kyau ga rayuwar mutane.
Gwamna Yusuf ya kuma kara da rokon al’ummar Bichi da su ci gaba da bai wa dan majalisar goyon baya gabanin zaben 2027.
Taron ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC da shugabannin siyasa, ciki har da wakilan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ‘yan majalisar tarayya da jami’an jam’iyya.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa tabbatar da ‘dan takarar da aka yi a Bichi babu kamarsa a fadin kasar nan dangane da tsari da taron al-umma.












































