A gaggauce: Farouk Ahmed da Gbenga Komolafe sun yi murabus, Tinubu ya miƙa sunayen waɗanda za su maye gurbin su ga Majalisar Dattawa domin tantancewa

imgonline com ua twotoone oW5ULAr2cY 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da naɗin sababbin shugabannin hukumomin kula da harkokin mai da iskar gas na ƙasa, bayan murabus ɗin Injiniya Farouk Ahmed daga Hukumar Kula da Harkokin Mai da ƙayyade farashi NMDPRA da Gbenga Komolafe daga Hukumar Kula da Harkokin Hako Mai da Iskar Gas ta Ƙasa NUPRC.

Buƙatar ta biyo bayan murabus ɗin kwatsam da manyan jami’an biyu suka yi, inda aka bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya naɗa su a shekarar 2021 domin jagorantar hukumomin da aka kafa ƙarƙashin Dokar Masana’antar Man Fetur.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a wata sanarwa cewa shugaban ƙasa ya rubuta wasiƙa zuwa Majalisar Dattawa, yana neman a hanzarta tantancewa da amincewa da Oritsemeyiwa Amanorisewo Eyesan a matsayin shugabar Hukumar Kula da Harkokin Hako Mai da Iskar Gas ta Ƙasa NUPRC, da kuma Injiniya Saidu Aliyu Mohammed a matsayin shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai da ƙayyade farashi NMDPRA ta Ƙasa.

Sanarwar ta nuna cewa mutanen biyu ƙwararru ne masu gogewa a fannin mai da iskar gas, tare da tarihin aiki a manyan mukamai a cikin masana’antar.

Karanta: ICPC ta tabbatar da karɓar ƙorafin Dangote kan shugaban hukumar NMDPRA, ta ce za a bincika ƙorafin yadda ya dace

Eyesan ta kammala karatun tattalin arziƙi a Jami’ar Benin, kuma ta yi kusan shekaru 33 tana aiki a Kamfanin Man Fetur na Ƙasa da rassansa, inda ta yi ritaya a matsayin mataimakiyar shugabar zartarwa mai kula da harkokin hako mai, tare da riƙe muƙamin babban manajan tsare-tsare da dabaru na kamfani a baya.

Shi kuwa Injiniya Saidu Aliyu Mohammed, wanda aka haifa a jihar Gombe a shekarar 1957, ya kammala karatun injiniyan sinadarai a Jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 1981, kuma a baya-bayan nan an bayyana shi a matsayin darakta mai zaman kansa ba na zartarwa ba a Kamfanin Makamashin Seplat, tare da riƙe manyan mukamai a matatun mai da kamfanonin gas na ƙasa.

Rahoton ya ƙara da cewa murabus ɗin Farouk Ahmed ya zo ne a daidai lokacin da attajirin Afirka kuma mai Matatar Mai ta Dangote, Aliko Dangote, ya zarge shi da aikata laifin da ka iya haifar da taɓarɓarewar tattalin arziƙi da cin hanci da rashawa, lamarin da ya ƙara jan hankali kan sauye-sauyen shugabanci a hukumomin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here