Tsarin Demokradiyyar Najeriya na cikin haɗari idan babu sahihin zaɓe – Jega

WhatsApp Image 2025 12 05 at 05.12.25 720x430

Tsohon shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa INEC Farfesa Attahiru Muhammad Jega, ya yi gargaɗin cewa mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya zai ci gaba da tangal-tangal muddin ba a ɗauki matakai na gaggawa ba wajen ƙarfafa sahihancin zaɓe da dawo da amincewar jama’a ga tsarin siyasa.

Da yake jawabi a matsayin babban bako mai jawabi a wajen taron jama’a da Jami’ar Tarayya Kashere (FUK) ta Jihar Gombe ta shirya a ranar Alhamis, Farfesa Jega ya gabatar da muƙala mai taken “Zabe da kyakkyawan shugabanci a Najeriya.

Ya ce duk da shekaru 26 da dawowar ƙasar ga mulkin farar hula a jamhuriya ta huɗu, har yanzu Najeriya na fama da ƙalubale wajen tabbatar da ingantacciyar demokuradiyya saboda kura-kurai da ke ci gaba da faruwa a tsarin zaɓe.

A cewarsa, sahihancin zaɓe shi ne ginshiƙin demokuradiyya mai inganci, domin kuwa dole ne zaɓe ya kasance mai ’yanci, gaskiya, bayyananniyar hanya, tsari mai inganci da bin doka.

Jega ya ce demokuradiyya ba za ta bunƙasa ba idan an ci gaba da samun karkatar da sakamakon zaɓe, tashin hankali, matsalolin jigilar kayan zaɓe, sayen kuri’u, raunin hukumomi, da kuma ƙaruwar tashe-tashen hankula a shari’ar zaɓe.

Ya bayyana cewa matsalar mulki a Najeriya na ƙara tsananta sakamakon cin hanci, nuna isa daga masu mulki, amfani da ’yan daba, da kuma tazara mai faɗi tsakanin jama’a da shugabannin siyasa.

Ya yi nuni da cewa akwai buƙatar ingantaccen tsarin dokokin zaɓe, hukumomin gudanar da zaɓe masu cikakken ’yanci da ƙwarewa, kundin rajistar masu zaɓe mai inganci, tsari mai gaskiya wajen tattarar sakamakon zaɓe, da kuma tsauraran dokoki kan kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe.

Jega ya yi kira da a kafa ƙungiya ta kasa baki ɗaya da za ta yi aiki kan sahihancin zaɓe domin tayar da ƙarfi wajen kawo sauye-sauyen da za su ƙarfafa demokuradiyya, su ƙara wa ’yan ƙasa kwarin gwiwa, tare da bunƙasa shugabanci mai nuna gaskiya da kula da jama’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here