Kotun tarayya ta kori ƙarar Bukola Saraki kan EFCC, ICPC da wasu

Saraki Saraki 750x430

Kotun Ƙoli ta tarayya da ke Abuja a ranar Talata ta kori ƙarar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya shigar domin neman kariya daga binciken da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta shirya yi a kansa.

Mai shari’a Mohammed Umar ne ya kori ƙarar bayan ganin takardar janye shari’ar da aka ajiye a cikin bayanan kotu, sannan kuma babu wani lauya da ya bayyana a gaban kotu lokacin da aka ci gaba da sauraren karar.

Saraki ya shigar da ƙarar ne tun a shekarar 2019, bayan da hukumar EFCC ta fara binciken yadda ya samu dukiyarsa tsakanin shekarun 2003 zuwa 2011 lokacin da yake gwamnan jihar Kwara.

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta kwace wasu gidajen sa da ke unguwar Ikoyi, Legas.

A ranar 10 ga Mayu, 2019, Saraki ya shigar da ƙarar biyu daban-daban, masu lamba FHC/ABJ/CS/507/2019 da FHC/ABJ/CS/508/2019, a gaban mai shari’a Taiwo Taiwo (mai ritaya), inda ya kalubalanci matakin EFCC.

Karin karatu: EFCC ta kuduri aniyar ƙarfafa haɗin gwiwa da ‘yan jarida a Kano wajen yaƙi da cin hanci

Ya haɗa da babban lauya na tarayya, sufeton ‘yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) a matsayin wadanda ake ƙara, tare da EFCC, hukumar ICPC da kuma hukumar kula da ɗa’ar ma’aikata (CCB).

Kotun a wancan lokaci ta bayar da umarnin dakatar da duk wani bincike da EFCC da sauran hukumomi ke yi, har sai an kammala sauraren karar, amma daga baya EFCC ta bukaci a mayar da shari’ar wata kotu daban.

Wannan ya sa aka tura ta a gaban wasu alkalai daban-daban har zuwa lokacin da aka sake watso da ita a watan Janairun 2023 saboda rashin ci gaba da shari’a yadda ya kamata.

Sai dai daga baya, lauyan Saraki ya sake neman kotu ta dawo da karar cikin jerin shari’o’i da ake ci gaba da saurare.

A ranar 28 ga Oktoban 2024, mai shari’a Inyang Ekwo ya amince da buƙatar sake fasalin ƙarar, lamarin da ya sa aka sake mayar da ita a gaban mai shari’a Umar.

Wannan hukuncin na baya-bayan nan na kotu ya zama ƙarshen ƙoƙarin Saraki na neman kariya daga binciken EFCC.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here