Babbar jojin Najeriya ta rantsar da sababbin lauyoyi 57 da suka samu matsayin SAN

imgonline com ua twotoone Ucryc8a1qJykMR 750x430 (1)

Babbar jojin Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, a ranar Litinin ya rantsar da lauyoyi 57 a matsayin manyan lauyoyin Najeriya (Senior Advocates of Nigeria, SAN) a kotun koli da ke Abuja.

Cikin wadanda suka samu karin girma akwai Aminu Gadanya da Abdulkarim Maude, lauyoyi masu kare shari’o’i daga jihar Kano.

Haka kuma, Maude yana jiran tantancewar majalisar dokokin Kano bayan da aka sanya sunan shi cikin wadanda za a nasa shi a matsayin kwamishina.

A wajen zaman musamman na kotun koli domin fara shekarar shari’a ta 2025/2026, Mai Shari’a Kekere-Ekun ta bayyana wannan karin matsayi a matsayin lokaci na tunani da sabunta alƙawari ga aikin adalci.

Ta yi kira ga sababbin SAN su kiyaye mutuncin wannan matsayi, tana gargadi cewa za a iya kwace shi idan an yi amfani da shi ba bisa ka’ida ba.

Ta kuma nuna Alihini ha manyan alkalai hudu da suka rasu a shekarar shari’a ta baya, ciki har da tsohon Alkalin Alkalai Muhammadu Lawal Uwais, tare da mika ta’aziyya ga iyalansu da kuma iyalan ma’aikatan shari’a da suka rasu a wannan lokaci.

Kekere-Ekun ta bayyana wasu muhimman gyare-gyare da aka samu a tsarin shari’a, ciki har da warware dukkan ƙorafe-ƙorafen da aka shigar gaban majalisar shari’a ta ƙasa (NJC), dainganta tsarin adana bayanan kotu ta hanyar internet da kuma samar da sabbin sassan binciken shari’a domin sauƙaƙa samun bayanai.

Haka kuma ta sanar da shirin ƙaddamar da tsarin amfani da Internet na gudanar da shari’a a duk faɗin ƙasa.

A rahotonta, CJN ta ce kotun koli ta saurari shari’o’i 2,280 ciki har da daukaka kara 560, tare da yanke hukunci 369 – abin da ya fi na bara wanda aka yi hukunci 247.

Ta kuma bayyana cewa kwamitin COTRIMCO ya ci gaba da haɗin gwiwa da hukumar EFCC da ta samu hukuncin laifuka 1,417 a 2025, da kuma hukumar ICPC wacce ta ƙaddamar da sababbin shari’o’i 43 tare da samun hukuncin laifuka tara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here