Jami’ar tarayya dake Dutse dake jihar Jigawa ta samu tallafin bincike na naira miliyan 27 daga asusun bincike na kasa TETfund domin gudanar da bincike kan sinadarin da ake amfani da shi wajen samar da iskar gas wanda zai yi aiki a matsayin madadin man fetur ga motoci da jiragen kasa.
Jagoran masu bincike Dokta Hafeez Yusuf Hafeez na sashin Physics na Jami’ar Tarayya Dutse ne ya bayyana hakan ga Jaridar FUD.
Dokta Hafeez ya ce amfani da sinadarin hydrocarbon a matsayin madadin man fetur wani fanni ne da ya kunno kai a duniyar kimiyya kuma binciken da aka yi na da nufin binciko wannan sabon yanki wanda albarkatunsa ruwa ne da hasken rana.
Solacebase ta ruwaito cewa tawagar masu binciken sun hada da Farfesa Abdulsalam Balarebe Suleiman, Farfesa Chifu Ndiklar, Dr. Jibrin Mohammed, Farfesa Rabia S.Salihu na BUK da kuma Dakta Ibrahim Muhammad na Jami’ar Jihar Sakkwato.
“Binciken sabon abu ne a Afirka amma ya sami ‘yanci sosai a Amurka, Faransa, Japan, Kanada da Jamus inda aka riga aka fara amfani da motocin da ke amfani da sinadarin hydrocarbon yayin da Japan ta ci gaba da samar da wutar lantarki da iskar gas,” in ji jaridar FUD.
”Dr. Hafeez ya ce binciken ci gaba ne na karatun digirin digirgir (Ph.D) wanda ya lashe mafi kyawun bincike na Afirka a Indiya saboda sabon salo na yankin ya kara da cewa babu wanda ke aiki a wannan fanni a halin yanzu a Afirka.
Jagoran masu binciken ya ce bukatar madadin man fetur ya zama abin damuwa a duniya saboda illar da man fetur ke haifarwa ga muhalli musamman sauyin yanayi da dumamar yanayi inda ya kara da cewa man da ake samarwa daga hasken rana da ruwa yana da arha.













































