An daina yin jarabawa a cibiyoyin da basu shirya ba-JAMB

Jamb
Jamb

Hukumar JAMB ta sanar da cewa cibiyoyi jarabawar wanda suka shirya dari bisa dari ne kadai zata yi amfani dasu wajen gudanar da jarabawar ta shekarar 2022.

Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da hukumar ta gama shirye-shiryen fara tantance cibiyoyin da za’a yi jarabawar ta shekarar 2022.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin shugaban hukumar ta ce hukumar ta yanke wannan hukunci ne bayan wata ganawa da suka yi ta intanet. Ganawar ta samu halartar manyan daraktocin hukumar da shugabannin hukumar shiyyoyi da jihohi da kuma jami’an sashen dake tantance cibiyoyin jarabawa.

An ruwaito Shugaban hukumar ta JAMB Farfesa Ishaq Oloyede na bayyana cewa, bayan kammala jarabawar ta shekarar 2021 sun gano cewa akwai cibiyoyin da basu shirya ba, amma an basu damar yin jarabawar, inda ya bayyana cewa a wannan karon hakan ba zata faru ba dole se an tabbatar da cewa cibiya ta shirya sannan za’a bata dama.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here