Gwamnatin Chadi ta ce ta yi afuwa tare da sakin ƴn tawaye 380 da suke zaman ɗaurin rai da rai a gidan yari saboda mutuwar tsohon shugaban ƙasar, Idriss Deby.
An kashe tsohon shugaban ƙasar shekara biyu da suka wuce a filin daga a ƙoƙarin yaƙar ƴan bindiga da ake kira Front for Change and Concord.
A watan Maris ne aka yanke wa ƴan tawaye sama da 400 hukunci saboda aikata laifukan ta’addanci da ɗaukan yara aikin soja da kuma cin zarafin shugaban ƙasa.
Ɗan tsohon shugaban ƙasar – Mahamat Idriss Déby – ya yi wa akasarinsu afuwa.
Mahamat Deby ya karɓi ragamar ƙsar bayan mutuwar mahaifinsa.
Sai dai afuwar ba ta shafi jagoran ƴan tawaye Mahamat Mahdi Ali ba wanda ake nema ruwa a jallo.












































