2023: Za Mu Fi Maza Tabuka Abin Azo A Gani, In Ji Yan Takarar Gwamna Mata a Najeriya

Women in politics
Women in politics

Yan takarar gwamna mata daga jam’iyyun siyasa daban-daban, a ranar Litinin sun yi alkawarin za su yi aiki fiye da takwarorinsu maza idan an zabe su a yayin zaben 2023 a Najeriya.

Sun kuma soki mafi yawan yan siyasa, musamman gwamnoni saboda gazawarsu na samar da romon demokradiyya ga mutane da suka zabe su.

Yan takarar gwamna matan sun fadi abin da ke zukatansu ne a Abuja yayin wani taro da yan jarida da Women Radio da Women in Business tare da tallafi daga United Nations Women (Nigeria) da Gwamnatin Kanada suka shirya.

Wakiliyar mata na UN, Beatrice Eyong, ta ce duk da cewa yawan mata da ke majalisa ya rubanya a duniya tun 1995 zuwa kashi 26.4 cikin dari, lamarin ba haka yake a Najeriya ba don raguwa ya ke yi tun 1999.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here