Ƴan sanda sun kama wani da ake zargin yana kera bindigogi ga ’yan ta’adda tare da yi musu safarar su zuwa Kwara

Police olopa new 750x430

Rundunar ƴan sanda a jihar Kwara ta tabbatar da cafke wani mutum daga Makurɗi da ake zargin yana kera bindigogi da kuma safarar su ga ’yan ta’adda da ke aiki a sassa daban-daban na jihar.

Haka kuma an kama wasu mutane da ake zargin su ke taimaka wa waɗannan miyagun mutane ta hanyar kai musu abinci, man fetur, magunguna da sauran kayayyakin bukata da suke amfani da su a maboyarsu.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Adekimi Ojo ne ya bayyana hakan ranar Jumaa bayan kammala taron masu ruwa da tsaki kan al’amuran tsaro a Ilorin.

Ya ce, an kama mutanen ne bayan samun bayanan leƙen asiri da suka nuna cewa suna haɗa kayan aikin harba bindiga tare da kai su zuwa dazukan da ’yan ta’adda ke buya domin gudanar da ayyukan barna.

Rundunar ta bayyana cewa an kama wani babban mai gyaran bindiga wanda ya dade yana samar wa ƙungiyoyin ta’addanci makamai da kayayyakin gyara, lamarin da ya taimaka wajen ƙara ƙarfafa su a hare-haren da suke kai wa al’umma.

Rundunar ta kara da cewa a halin yanzu ana ci gaba da bincike domin gano sauran mutane da ke da hannu a safarar makamai da kayan tallafi ga ’yan ta’adda, tare da tabbatar da cewa duk masu hannu a laifin za a gurfanar da su.

Rundunar ta yi kira ga al’umma da su rika game da bayyana duk wata ƙungiya ko mutum da ake zargin yana hulɗa da ’yan ta’adda, domin taimakawa wajen daƙile ayyukan ta’addanci a jihar da ma ƙasar baki ɗaya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here