Zulum ya raba motocin Sintiri guda 63 ga hukumomin tsaro a Jihar Borno

IMG 5976 750x430

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Talata ya raba motocin Sintiri guda 63 ga hukumomin tsaro da sassa daban-daban na tsaro domin ƙarfafa ayyukan tsaro a birnin Maiduguri da kewaye.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa, rabon motocin na da nufin inganta zirga-zirga, hanzarta amsa amsa kiran gaggawa da ƙarfafa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro da ke aiki a cikin babban birnin jihar.

Daga cikin motocin 63 da aka raba, an bai wa sassa 10 na ƙungiyar Civilian Joint Task Force (CJTF) motoci 30, Rundunar Rapid Response da Anti-Social Vices motoci 16, hukumomin paramilitary motoci 10, ƙungiyar mafarauta motoci 6, sannan hukumar hana fataucin mutane (NAPTIP) ta samu mota ɗaya.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa wannan mataki wani ɓangare ne na jajircewar gwamnatinsa wajen ƙarfafa tsarin tsaro a jihar domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa rundunonin soji, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro da kawar da ayyukan ta’addanci gaba ɗaya a yankin.

Zulum ya yaba wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da hafsoshin tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi wajen magance matsalar ta’addanci a arewa maso gabas.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya kuma bayyana cewa tun daga shekarar 2019, gwamnatin Zulum ke ci gaba da raba motocin tallafi ga hukumomin tsaro domin taimaka musu a ayyukansu na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here