Yanzu-yan: Tinubu ya rantsar da Taiwo Oyedele a matsayin karamin ministan kudi

taiwo oyedele tax

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Taiwo Oyedele a matsayin ƙaramin ministan kuɗi.

An gudanar da bikin rantsarwar ne a taƙaice a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin.

Tun da fari jami’an tsaro na fadar shugaban ƙasa sun tantance Oyedele tare da matarsa da misalin ƙarfe 2:09 na rana, inda sabon ministan ya sanya rigar kwat mai launin shuɗi mai duhu, yayin da matarsa ta sanya kayan gargajiya masu launin fari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here