Rundunar ƴan sanda ta sake dawo da bayar da izinin amfani da baƙin gilashin mota

IGP Kayode Egbetokun PMF 750x430

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sake farfado da bayar da lasisin yin amfani da baƙin gilashin mota “Tinted Glass” a hukumance a fadin kasar, biyo bayan umarnin babban sufeton ‘yan sandan kasa Kayode Adeolu Egbetokun.

Matakin ya nuna komawa ga tsarin da aka tsara bayan shekaru na da aka rika damuwa da karuwar korafe-korafe game da cin zarafin da masu amfani da baƙin gilashin motar ke yiwa sauran masu ababen hawa.

A cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Talata mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce sabon tsarin na da nufin samar da daidaito a tsakanin halalcin amfani da baƙin gilashin ababen hawa da kuma bukatar tabbatar da tsaron kasa.

Za a gudanar da shirin a yanzu ta hanyar ingantaccen tsarin internet, wanda aka tsara don inganta gaskiya, da rikon amana, da inganci.

Karanta: Gobara ta lalata Kasuwar Terminus a Jos

Matakin dai ya zo ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan yadda ake cin zarafin masu ababan hawa da kuma yadda ake yin amfani da su wajen aikata laifuka kamar su garkuwa da mutane, fashi da makami, da kuma badakala”. A cewar ‘yan sanda, irin wadannan motoci sukan hana ganin jami’an tsaro tare da ba da kariya ga masu aikata laifuka.

Rundunar ta ce, ana buƙatar masu neman izinin amfani da shi da su tabbatar suna da Lambar shaidar zama ɗan Ƙasa (NIN) da Lambar Shaida ta Haraji (TIN) da sauran muhimman takardu, kuma za a ba da izini tare da lambobin QR cikin sa’o’i 72.

Domin tabbatar da an samu sauyin yanayi, rundunar ta sanar da wa’adin kwanaki 30 daga ranar 1 ga Mayum 2025, domin fara aiwatar da aikin a wannan lokaci, kuma jami’an ‘yan sandan da aka samu da hannu wajen karbar kudi ko cin zarafi a karkashin inuwar jami’an tsaro za su fuskanci hukuncin ladabtarwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here