Sanata Orji Uzor Kalu, wanda ke wakiltar Abia ta Arewa, ya ce tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi ƙarya lokacin da ya musanta neman wa’adin mulki na uku, yana mai cewa tsohon shugaban ƙasar ne da kansa ya sanar da shi wannan niyya.
A cewar Kalu, Obasanjo ya taɓa gayyatarsa zuwa fadar shugaban ƙasa lokacin yana mulki domin tattauna shirin gyara kundin tsarin mulki da nufin ƙara wa kansa wa’adin mulki.
Ya ce wannan magana ta saba da abin da Obasanjo ya faɗa a taron tattaunawar dimokuraɗiyya da Cibiyar Tattaunawa ta Goodluck Jonathan ta shirya a birnin Accra a watan Satumba, inda tsohon shugaban ya musanta zargin neman wa’adi na uku.
Kalu ya bayyana hakan ne a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels, inda ya ce Obasanjo bai faɗi gaskiya ba game da batun.
Ya ƙara da cewa mutane da dama da suka kasance cikin gwamnati a wancan lokaci suna raye kuma sun san abin da ya faru.
Labari mai alaƙa: Idan ina so na yi wa’adi na uku, da zan samu — Cewar Obasanjo
Tsohon gwamnan jihar Abia ya kuma yi zargin cewa a lokacin, wani sanata ya kawo naira miliyan 50 don raba wa gwamnoni domin samun goyon bayansu ga gyaran kundin tsarin mulki, amma shi ya ƙi karɓa saboda ya yi rantsuwa da Littafi Mai Tsarki cewa zai yi mulki na shekaru takwas kacal.
Kalu ya ce rikicinsa da Obasanjo ya samo asali ne bayan ya sanar da shugabannin ƙasashe kamar Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu da George Bush na Amurka, har ma da Nelson Mandela, game da shirin tsohon shugaban ƙasar na neman wa’adin mulki na uku.
Ya bayyana cewa duk da cewa Obasanjo ya samu nasarar jawo wasu gwamnoni su goyi bayansa, wasu daga cikinsu ciki har da shi sun tsaya kan matsayinsu na kin amincewa da yunƙurin tsawaita mulki.
Kalu ya kammala da cewa bai kamata a gina Najeriya a kan ƙarya da ta fito daga manyan mutane ba, domin hakan na lalata amincin ƙasa da dimokuraɗiyya.












































