Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), mai ritaya ya bayyana takaicinsa kan rushe zaɓen shugaban ƙasar na ranar 12 ga watan Yunin 1993.
Yayin da yake jawabi a wurin bikin ƙaddamar da littafin da ya rubuta kan tarihin rayuwarsa mai taken “A Journey in Service”, a Abuja, babban birnin ƙasar, IBB ya ce in da zai samu wata damar da ya tabbatar da zaɓen.
Karin karatu: INEC ta ba da shawarar kafa kotu ta musamman kan laifukan zabe
Zaɓen na June 12 – wanda manyan ƴantakara biyu suka yi kankankan, Mashood Abiola na jam’iyyar SDP da Bashir Usman Tofa na jam’iyyar NRC – Abiola ne ya yi nasara.
“Na yi nadamar rushe zaɓen June 12, na kuma ɗauki alhakin matakin – wanda aka ɗauka a zamanin mulkina, na kuma ɗauki hakan a matsayin kuskure.”
BBC