Matsalar rashin ingancin sadarwa: Kwamitin Majalisar Wakilai ya gayyaci shugabannin Airtel, MTN, Glo

Reps Reps

Wani kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai ta Tarayya ya gayyaci manyan shugabannin kamfanonin sadarwa da ke aiki a Najeriya, sakamakon matsalar rashin ingancin sadarwa da ake fama da shi a sassan ƙasar.

Kwamitin da aka kafa domin gudanar da bincike kan rashin ingancin ayyukan sadarwa ya bayar da wannan sammaci a ranar Laraba, inda ya buƙaci shugabannin kamfanonin MTN Nigeria, Airtel Nigeria, Globacom (Glo), Mafab Communications Limited da sauran masu samar da ayyukan sadarwa su bayyana a gabansa ranar 28 ga Oktoba.

Kwamitin ya ɗauki wannan mataki ne bayan ’yan majalisar sun nuna rashin gamsuwarsu da zargin cewa manyan shugabannin kamfanonin sun gaza amsa gayyatar da aka yi musu a baya.

Kwamitin ya kuma umarci Hukumar Kula da Sadarwa ta Ƙasa (NCC) da ta tabbatar da cewa shugabannin kamfanonin sun bi umarnin gayyatar.

’Yan majalisar sun buƙaci kamfanonin sadarwar su yi bayani kan ci gaba da tabarbarewar ingancin ayyukansu, lamarin da ya kawo cikas ga sadarwa da harkokin kasuwanci ga miliyoyin masu amfani da ayyukan sadarwa da ’yan kasuwa a faɗin ƙasar.

Kwamitin ya yi barazanar bayar da sammacin kama duk wani shugaban kamfani da ya ƙi bayyana a gabansa.

Shugaban kwamitin, Olumide Osoba, ya ce harkar sadarwa na taka muhimmiyar rawa a tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce ɓangaren ya wuce samar da damar yin kira da amfani da intanet, ya zama wani muhimmin ɓangare na mu’amalolin kasuwanci, ciki har da biyan kuɗi ta na’urorin POS.

Ya bayyana cewa harkokin kasuwanci, ayyukan kuɗi da sauran muhimman ayyukan tattalin arziki sun dogara matuƙa da ingantattun hanyoyin sadarwa, yana mai cewa tabarbarewar ayyukan sadarwa batu ne da ya shafi ƙasa baki ɗaya.

Osoba ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne domin bincika yawan koke-koken masu amfani da ayyukan sadarwa da kuma gano ainihin dalilan da ke haddasa rashin ingancin ayyukan.

Wani ɗan majalisa daga jihar Abia, Ibe Osonwa, ya ce gazawar shugabannin kamfanonin wajen bayyana a gaban kwamitin na nuna rashin mutunta Majalisar Dokoki.

Osonwa ya ce bai kamata kamfanonin da ke samun riba mai yawa daga kasuwar Najeriya su yi watsi da gayyatar majalisa ba, musamman idan binciken ya shafi ingancin ayyukan da suke samarwa ga abokan cinikinsu da kuma tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.

A ranar Talata, Hukumar NCC ta bayyana cewa an biya masu amfani da ayyukan sadarwa miliyan 75 diyya ta hanyar ƙarin kuɗin kati sakamakon rashin ingancin sadarwa a shekarar 2026.

Hukumar ta ce ana sa ran wannan mataki, wanda aka aiwatar a ƙarƙashin tsarin biyan diyya ga masu amfani da ayyukan sadarwa, zai taimaka wajen inganta ingancin sadarwa ga masu amfani da su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here