Amurka ta umarci jami’an ofishin jakadancinta da iyalansu su bar Saudiyya

Download 750x430

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta umarci wasu jami’an diflomasiyyarta da iyalansu da ke Saudiyya su fice daga kasar, yayin da take shirin janye iyalan jami’anta daga wasu ofisoshin jakadancinta da ke yankin Gabas ta Tsakiya, kamar yadda jami’an Amurka suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Umarnin ya zo ne a daidai lokacin da hare-hare a Saudiyya suka yi sanadin mutuwar a kalla mutum guda tare da jikkata wasu takwas a wani filin jirgin sama na fararen hula da ke Dammam, yayin da wasu mutane biyu suka mutu sakamakon harin jirgi mara matuki a wani wurin hakar mai.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, Tommy Pigott, ya bayyana a wani sako da ya wallafa a shafin X cewa ma’aikatar ta bayar da umarnin ficewar “ma’aikatan gwamnatin Amurka da ba sa gudanar da ayyukan gaggawa da kuma iyalansu da ke Saudiyya kawai”, sakamakon hare-haren da mayakan Houthi masu alaka da Iran da ke Yemen ke kai wa wuraren fararen hula a kasar.

A cikin watannin baya-bayan nan, Washington ta sake tura wasu jami’an diflomasiyya zuwa yankin, bayan janye da dama daga cikinsu a lokacin da Tehran ta fara kai hare-hare kan cibiyoyin Amurka, bayan barkewar yakin Amurka/Isra’ila da Iran a karshen watan Fabrairu.

Pigott ya ce, “Mayakan Houthi da Iran ke goyon baya sun kara tsunduma cikin rikici da Saudiyya, ciki har da kai hare-hare kan filayen jiragen saman fararen hula da sauran muhimman ababen more rayuwa, lamarin da ya jawo asarar rayukan fararen hula tare da kawo babban cikas ga zirga-zirgar matafiya.”

Jami’an Amurka hudu sun shaida wa Reuters cewa ofisoshin jakadancin Amurka da ke wasu kasashen yankin Tekun Fasha za su kuma bayar da umarnin ficewar iyalan jami’ansu. Sai dai Pigott ba ta yi karin bayani kan sauye-sauyen da za a yi a sauran ofisoshin jakadancin da ke wajen Saudiyya ba.

Sabon matakin janye jami’an ya biyo bayan karuwar fada a Yemen, wanda ya bude wani sabon fagen rikici a yakin yankin da ya samo asali daga yakin Amurka/Isra’ila da Iran.

Rikicin yankin baki daya ya kawo cikas ga kasuwancin makamashi na duniya, tare da jefa tattalin arzikin kasashen yankin Tekun Fasha cikin matsin lamba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here