Kungiyar likitocin Najeriya ta NARD ta dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai.
Mambobin kungiyar ta NARD sun shiga yajin aikin ne a ranar Litinin 26 ga watan Agusta saboda sace mamban kungiyar Dokta Ganiyat Popoola-Olawale sama da watanni 7.
Amma bayan taron majalisar zartarwa ta kasa (ENEC) na musamman da ta gudanar a ranar Lahadi, 30 ga watan Agusta, 2024, kungiyar ta sanar da janye yajin aikin.
NARD ta ce ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne tare da sanya ido sosai kan abubuwan da ke faruwa tare da jawo hankalin masu ruwa da tsaki don ganin an sako yar kungiyar da aka sace cikin gaggawa.
Sanarwar ta samu sa hannun shugaban kungiyar Dokta Dele Abdullahi Olaitan, Sakatare Janar, Dokta Anaduaka Christopher Obinna, da Dokta Egbe John Jonah.
Ya yaba da irin gudumawar da hukumomin gwamnati daban-daban suka bada, da kuma sabon alkawarin da suka yi na kubutar likitan da aka sace.
An sace Dr Popoola-Olawale ne a ranar Laraba 27 ga Disamba, 2023 a cikin rukunin gidajen manyan ma’aikata na National Eye Center Kaduna.
An sace ta ne tare da mijinta, shugaban Squadron Nurudeen Popoola da kuma kanin mijinta {Folaranmi Abdul-Mugniy.
Daga baya an saki mijin a ranar 7 ga Maris 2024.
Dr Popoola da Folarin har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane.
An tsince ta ne tare da mijinta, shugaban Squadron Nurudeen Popoola da kuma kanin mijin {Folaranmi Abdul-Mugniy, dalibin Cibiyar Fasahar Sojan Sama (AFIT) wanda ke tare da su}.
Bayan ƙoƙari da shawarwari da yawa, an saki mijin a ranar 7 ga Maris 2024.
Dr Popoola da Folarin har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane.