Kungiyar Kwankwasiyya ta gargadi majalisar dokokin da gwamnatin Kano kan shirin tsige mataimakin gwamna

Aminu Abdussalam Gwarzo 750x430

Kungiyar Kwankwasiyya ta gargadi gwamnatin Kano da majalisar dokokin jihar Kano kan duk wani yunkuri na tsige mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, tana mai cewa irin wannan mataki na iya kara rarrabuwar kawuna a siyasa tare da tauye amanar da al’ummar jihar suka bai wa wannan gwamnati.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a ranar Alhamis majalisar dokokin Kano ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan, Aminu Abdussalam Gwarzo, bisa zargin karkatar da kudi, tare da ba shi wa’adin makonni biyu domin ya mayar da martani kan takardar sanarwar da aka aike masa.

Lamarin sauya sheka da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da mafi yawan ‘yan majalisar dokokin jihar suka yi zuwa APC bai yi wa kungiyar Kwankwasiyya dadi ba, wadda Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta.

Sai dai mataimakin gwamnan ya ki barin jam’iyyar NNPP ta kungiyar Kwankwasiyya.

A cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar, Dakta Habibu Sale Mohammed ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana shirin tsige mataimakin gwamnan a matsayin abin damuwa, tare da kira ga ‘yan siyasa a jihar da su guji daukar matakan da za a iya fassara su a matsayin na siyasa.

Ya bayyana cewa al’ummar Kano na bibiyar abubuwan da ke faruwa a kusa, yana mai cewa akwai karuwar damuwa kan cewa shirin tsige mataimakin gwamnan na iya kasancewa ya fi karkata ga siyasa maimakon bukatar doka.

A cewarsa, ko da yake kundin tsarin mulki ya tanadi hanyoyin sa ido na majalisa kan ayyukan gwamnati, tsige mukami na daga cikin manyan iko da ‘yan majalisa ke da shi, don haka bai kamata a yi amfani da shi domin biyan bukatar siyasa ba.

Habibu Sale Mohammed ya kuma tunatar da shugabannin jihar cewa amanar da ta kai wannan gwamnati kan mulki ta samo asali ne daga kokarin hadin gwiwar dubban magoya bayan kungiyar Kwankwasiyya a kananan hukumomi 44 na jihar.

Ya jaddada cewa nasarar da ta samar da wannan gwamnati ba ta mutum guda ba ce, illa hadin kai, sadaukarwa da biyayya tsakanin mambobin kungiyar.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa kakakin ya gargadi cewa duk wani mataki da za a dauka wanda za a ga kamar an nufi manyan mutane a cikin gwamnati na iya aika sakon da bai dace ba ga magoya bayan da suka yi aiki tukuru wajen samun nasarar zabe.

Ya kuma bukaci ‘yan majalisar dokokin jihar Kano da su gudanar da nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu cikin taka tsantsan da ‘yancin kai, yana mai cewa ikon majalisa ya fito ne kai tsaye daga hannun al’umma.

Habibu Sale Mohammed ya kara gargadin cewa duk wani mataki na siyasa da za a dauka wanda za a ga kamar tsanantawa ne na iya haifar da tashin hankali a cikin yanayin siyasar jihar.

Ya kara da cewa kungiyar Kwankwasiyya na nan kan bakanta na tabbatar da zaman lafiya, dorewar dimokuradiyya da kare amanar siyasar da al’ummar jihar Kano suka bayar.

Ya bayyana cewa a wannan lokaci mai muhimmanci, dole ne duk masu ruwa da tsaki a siyasa su yi aiki cikin natsuwa da hikima, suna tuna sadaukarwar miliyoyin magoya bayan da suka hada karfi wajen kawo wannan gwamnati kan mulki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here