Hukumomin Iran sun fara kafa kyamarori a wurin da mutane suke taruwa domin gano matan da ke yawo ba tare da hijabi ba, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.
Duk macen da aka samu ba ta sanya hijabi ba za a “aika mata saƙon jan kunne,” in ji ‘yan sanda.
Wanda haka a cewarsu “zai rufe bakin masu adawa da wannan doka”.
Zanga-zanga ta mamaye Iran a bara bayan ‘yan sanda sun kashe wata matashiya mai suna Mahsa Amini, wata Baƙurdiya da aka zarga da karya dokar sanya hijabi.
Tun bayan mutuwar Mahsa, mata da yawa ke sanya hijabi musamman waɗanda ke zaune a manyan birane.













































