Gwamnatin Kano ta ƙuduri aniyar ɗaukar mataki yayin da masu sana’ar Achaba da aka haramta suka sake bayyana

okada riders2

Gwamnatin jihar Kano ta nuna damuwa game da karuwar ayyukan masu babur na haya da ake kira Achaba a fadin jihar, tare da bayyana cewa za ta dauki matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

A baya dai gwamnatin ta taba haramta ayyukan Achaba a ranar 24 ga Janairu, 2013, lokacin da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da dokar haramta su sakamakon jerin hare-haren tsaro da suka auku a Kano, ciki har da harin da ya kai ga tawagar marigayi Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.

Dokar ta kuma sake dawowa a shekarun 2017 da 2020 a matsayin wani bangare na matakan tabbatar da tsaro a jihar.

Waiya ya bayyana cewa rahotannin leƙen asiri sun tabbatar da cewa ayyukan Achaba sun sake karuwa a wasu yankunan birnin Kano da kuma wasu unguwannin makwabtaka da kananan hukumomi na kan iyaka.

Sanarwar ta ce duk da haramtawar da ta shafe lokaci, wasu mutane sun koma amfani da babura a matsayin sufuri, abin da ke haifar da kalubalen tsaro da ba za a yi watsi da su ba.

Kwamishinan ya ce gwamnati na aiki tare da jami’an tsaro domin shawo kan lamarin, tare da samar musu da duk abin da ake bukata domin tabbatar da ingantaccen aiki.

Ya kara da cewa gwamnati na duba shawarwarin jama’a kan karfafa sa ido, ciki har da sanya ido a hanyoyin shiga da fita daga jihar, a matsayin wani bangare na tsarin nazari da amsa matsalolin tsaro.

Waiya ya gode wa jama’ar Kano kan jajircewarsu, hadin kansu da kuma kishin kasa, yana mai cewa gudummawarsu na taimakawa wajen karfafa kokarin gwamnati na dakile matsalolin tsaro.

Sanarwar ta jaddada cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da jajircewa wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar.

Gwamnatin ta kuma bukaci jama’a da su kasance masu lura, su rika bayar da rahoton duk wani abin da suka ga yana da ban shakka, tare da hada kai da jami’an tsaro domin dakile dawowar ayyukan A-chaba a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here