Gwamnatin jihar Kano, ta zargi jam’iyyar APC da yunkurin bayar da cin hanci a kan shari’ar zabe

Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf

Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Baba Halilu Dantiye, ya fitar ta zargi APC da kokarin bayar da cin hancin ta hannun wani lauya.

Mai shari’ar da take jagorantar kotunan shari’oin zaben yan majalisar tarayya da na jiha a Kano, Jostis Flora Azinge, ce ta bayyana cewa, wani babban Lauya mai mukamin SAN yayi yunkurin bata cin hanci a kan shari’ar zaben, sai dai bata bayyana sunan babban lauyan ba.

Hakan ta sa gwamnatin Kanon yin kiran a gudanar da bincike kan lamarin musamman ga hukumomin da abin ya shafa, saboda zargin cewa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, jigo ne cikin mutanen da ake zargi da bayar da cin hancin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here