Ya ku `yan uwana yan Najeriya, Ina cike da farin ciki a yayin da nake wa Ilahirinmu, matasa da tsofaffi maraba da shigowa sabuwar shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu. Dole ne mu daga Hannuwanmu sama mu gode wa Allah madaukakin Sarki saboda albarkar da Ya yi wa kasar mu da kuma rayukan mu a cikin shekarar da ta gabata wato shekara ta dubu biyu da ashirin da uku.
Ko da yake Shekarar da ta gabata na kunshe da kalubale da dama, amma duk da haka an yi abubuwan alheri masu yawa, Ciki har da mika mulki daga tsohuwa zuwa sabuwar gwamnati cikin lumana, wadda hakan alama ce da ke nuna irin gagarumin cigaban da demokaradiyarmu mai shekaru ashirin da hudu a jere ta samu
Shekara ce wacce ku al’ummar wannan kasa mai Albarka kuka amince min da in jagorance ku, kan bayyanannen kudiri na yin gyara ga kasar nan, da yin garambawul a fannin tattalin arzikinta, da inganta tsaro a iyakokin kasarmu da farfado da masana`antun mu, da inganta noma, da cigaba na bai-daya, sannan in dora kasa a tafarkin cigaba mai dorewa ta yadda mu da `yan baya za mu yi alfahari da ita.
Aikin gina ingantacciyar kasa mai dauke da al’ummar da take kishin kowanne dan kasa, shine makasudin tsayawata takarar shugaban kasa. Kuma shine taken yakin neman zabena wato SABUNTA-FATA-NA-GARI a kansa kuka zabe ni a matsayin shugaban kasar mu don na tabbatar da shi.
Daukacin abubuwan da na gudanar a Ofis, kama daga matakan da na dauka, da tafiye-tafiye na zuwa kasashen waje tun daga ranar ashirin da tara ga watan Mayu na shekara ta dubu biyu da shirin da uku duk na yi su ne domin amfanin kasar mu da cigabanta.
A cikin watanni bakwai da suka gabata na gwamnatin mu, na dauki wasu tsauraran matakai da suka zama tilas domin ceto kasar mu daga mummunan yanayi. Daya daga cikin wadannan matakan shine cire tallafin mai wanda ya zama wani nauyi ko tarnaki ga kasar nan na tsawon shekaru arbain da biyu, da kuma cire damar da wasu `yan tsirarru suke da ita a harkar hada-hadar kudin kasashen waje, wadda wasu shafaffu da mai ne kawai a cikin mu ke cin gajiyarta. Ko shakka babu wadannan matakan sun kawo matsi ga daidai kun mutane da iyalai da kuma kasuwanci.
Ina sane da cewa tattaunawar da ta zama ruwan dare a wannan lokaci ita ce ta tsadar rayuwa da hauhauwar farashin kayan masarufi wadda ya zarce kashi ashirin da takwas cikin dari ga kuma rashin aikin yi ga wasu yan kasa
Kama daga manyan cibiyoyin kasuwanci na Lagos zuwa cikin birnin Kano har zuwa loko-loko na gaɓar teku da ke Bayelsa ina jin koke da ƙorafin `yan Najeriya masu aiki dare da rana domin neman abinda za su ciyar da iyalansu
Ina sane da abubuwan da suke damunku wadanda ku ka bayyana da wadanda ma ba ku bayyana ba. Na san wasu ƴan ƙasa sun fara tambayar shi a haka wannan gwamnatin take son ta sabunta fata na-garin na mu?
Ya ku `yan uwana ƴan Nijeriya, ina kira gare ku ku amince da ni. yarda da ni. Na san wannan lokaci ne da ake cikin wahala, amma kada mu sake mu yi kasa a guiwa saboda babu wata wahala dake dauwama. Mun shirya wa wannan lokacin kada mu tsorata, kada mu raunana. Ya kamata kalubalen tattalin arzikin da muke fuskanta yau ya kara mana kwarin gwiwa kuma ya sa mu kara so da imani ga kasar mu Najeriya. Ya kamata matsalolin da muke fuskanta su sanya mu kara jajircewa wajen gina kasa. Halin da muke ciki yanzu yasa mu kara dagewa ta yadda shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu za ta amfani duk yan kasa.
Tun lokacin da gwamnatinmu ta karbi ragamar mulki ake samun gagarimin ci gaba ta fuskar tsaron kasa, mun kubutar da da dama cikin wadanda aka yi garkuwa dasu daga hannun masu garkuwa. Duk da cewa ba zamu iya bugun kirjin mu ce mun shawo kan duk matsalolin tsaro ba, amma muna aiki tukuru domin samar da zaman lafiya a gidajen mu da wuraren aiyukanmu da lungu da sakon mu.
Bayan mun samar da hanyoyin farfado da tattalin arzikin kasa cikin watanni bakwai na shekara ta dubu biyu da ashirn da uku, yanzu mun shirya domin samar da haka a duk fannoni.
Ba da dadewa ba a taron sauyin yanayi na COP28 da akayi a watan Disamba a Dubai, ni da Shugaban Gwamnatin Jamus ,Olaf Schlz muka kulla yarjejeniyar yin aiki cikin gaggawa domin kammala aikin da kamfanin Siemens ke gabatarwa wanda zai samar da wutar lantarki zuwa ga Gidaje da wuraren kasuwanci a karkashin shirin Shugaban kasa wadda aka soma a shekara ta dubu biyu da Goma sha takwas.
Baya ga wannan muna shirin kaddamar da wasu ayyukan shimfida layukan samar da wutar lantarki da kuma inganta tashoshin samar da wutar a ko’ina a fadin kasar nan.
Gwamnatin da nake jagoranta ta fahimci cewa babu wani cigaba da za a samu muddin wutar lantarki bata wadata ba. A cikin shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu zamu kara hobbasa wajen soma tace danyen mai a matatar mai ta Fatakwal da ta Dangote wadanda zasu soma aiki gadan-gadan.
Domin tabbatar da samar da abinci da tsaro zamu gaggauta noma hekta dubu dari biyar na masara da Shinkafa da alkama da dawa da sauran hatsi. Mun kuma kaddamar da noman rani a filin da ya kai hekta dubu dari da ashirin a jihar Jigawa a watan Nuwamban da ya gabata a karkashin shirinmu na bunkasa noman alkama.
A wannan shekarar za mu yi hobbasa wajen ganin cewa duk wasu batutuwa na kudi da haraji da suka kamata a Sanya su bisa tsari an yi su yadda ya dace saboda kada a samu koma baya. A duk wata tafiya da nayi zuwa kasashen waje, sakon da nake bayarwa shi ne Najeriya a shirye take domin yin kasuwanci da kowa.
Zan yanke duk wani abu da zai kawo tarnaki ga kasuwanci a kasar nan kuma ba zan yi kasa a gwiwa ba wajen kawar da duk wani abu da zai hana Najeriya zama cibiyar kasuwanci ga masu son zuba jari daga nan cikin gida da kuma kasashen waje.
A cikin kasafin kudi na shekara ta dubu biyu da Ashirin da hudu dana gabatar a gaban majalisar dokokin kasa na bayyana manufofi guda takwas da gwamnatina tasa a gaba wadanda suka hada da tsaron kasa ciki da waje, da samar da aiyuka da inganta kasuwanci da samar da daidaito a zuba jari, da rage talauci da kuma inganta zamantakewa. Saboda mun dauki tsarin cigaban mu da matukar mahimmanci, kasafin kudin mu na shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu ya nuna karara mahimmancin da muka bai wa cimma burin mu a gwamnatance.
Za mu yi aiki tukuru domin tabbatar da ganin cewa duk dan Najeriya ya amfana da wannan gwamnatin. Har marasa karfi duk babu wadda za a bari a baya. A cikin wannan tsarin zamu gabatar da sabon tsarin Albashi mafi karanci ga hazikan ma`aikatan mu a cikin wannan Shekaran. Ba wai kawai abu ne daya kamata a yi saboda tattalin arziki har ma saboda dacewarsa a babin kyautatawa da kuma a siyasance.
Nayi rantsuwa cewa zanyi iya kokari na wajen bauta wa kasan nan a koda yaushe kamar yadda na fada a baya, don haka ba zan daga kafa ga duk wani wanda na bai wa mukami ba idan bai yi aiki yadda ya dace ba.
Don haka ne na samar da ofishi na musamman a ofishin shugaban kasa da zai rinka sanya ido kan manufofi da tsaretsaren gwamnati ya kuma tabbatar da ganin cewa anyi aiki yadda ya dace ta yadda gwamnati za ta inganta rayuwar alummar mu.
Tuni muka tsara hanyar bin diddigin ayyukan masu rike da muƙamai wanda zai fara aiki a kashin farko na sabuwar shekara. Ta haka za mu gane masu makoma a gwamnatina a cikin masu rike da madafun iko
Ya ku yan uwana yan Najeriya, bubban buri na a matsayina na Sanata a jamhuriya ta uku da kuma Gwamnan Lagos na tsawon shekaru takwas da kuma yanzu a shugaban wannan kasa mai dumbin albarka shine in gina kasa wacce za’a yi adalci ga kowa sannan a rage rashin daidaito a tsakanin alumma. Na kuma yi na`am da masu arziki suci moriyar arzikinsu da suka mallaka ta hanyar halal. Mun gamsu da cewa duk wani dan Najeriya da ya yi aiki tukuru yana da damar samun cigaba a rayuwa. Dole ne a nan in kara da cewa Allah ya hallicce mu da baiwa daban daban don haka ba dole ne dukkan ninmu mu samu sakamako iri daya ba idan muka yi aiki tukuru, amma gwamnatin mu, a cikin shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu zuwa gaba za tayi aiki domin bai wa kowanne dan kasa dama domin ya samu cigaba.
Domin sabuwar shekarar ta amfani dukkan mu, a matsayin mu na yan adam dole ne mu shirya mu yi namu kokarin. Aikin gina kasa mai albarka ba aikin shugaban kasa ko gwamnoni da ministoci da yan majalisa ko kuma jami`an gwamnati kawai ba. Makomar mu ta na da alaka da juna a matsayin mu na yan kasa daya wato Najeriya. Ko da Yarukan mu da aladun mu da Addinai ba daya bane bai kamata mu rinka samun rashin jituwa ba.
Acikin wannan sabuwar shekarar ya kamata a matsayin mu na yan Najeriya mu yi aiki tare domin samar da zaman lafiya da cigaba da kuma daidaito a kasar mu. Ina kuma kira ga abokan hamayyar siyasa ta a zaben daya gabata, cewa zabe ya wuce, yanzu lokaci ne daya kamata mu yi aiki tare domin cigaban kasar mu.
Dole ne mu bari fitilar da kowanne acikin mu yaro da babba mace da namiji ke dauke da ita, ta cigaba da haskaka hanyar mu ta zuwa ga nasara.
Ina muku barka da shiga Sabuwar Shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu.
Allah ya Albarkaci Najeriya.
Bola Ahmed Tinubu,GCFR
1 JANAIRU 2024.