Dan asalin jihar Kano, Abdul Yassar Yahaya Musa ya zama daya daga cikin ’yan takara hudu da suka lashe gasar kacici-kacici ta kasa ta a darasin Kwamfuta ta shekara-shekara.
Sakataren kungiyar Nigerian Computer Society reshen jihar Kano, Malam Lukman Bayero, shi ne ya shaida wa jaridar Solacebase a ranar Asabar cewa dalibai biyu daga makarantun sakandare 35 da ke Kano suka halarci gasar kacici-kacicin.
“Wannan shi ne karon farko da muka samu wanda ya yi nasara a gasar da aka fara sama da shekaru ashirin da suka wuce,” in ji Bayero.
”Rijistar gasar ana bude ta ne a watan Maris kuma ana iya shiga ta adireshin Internet wato www.ncs.org.ng”

Ya kuma bayyana cewa duk mutane hudun da suka yi nasara za a basu lambar yabo a ranar 2 ga watan Agustan shekarar nan da muke ciki ta 2022 a Abeokuta dake jihar Ogun.












































